✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (5)

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a…

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.

 

Gaba daya dai abin nufi a nan, a duk sa’ar da aka samu al’umma tana umarni da kuma aikata kyawawan ayyuka, to wannan al’ummar za ta yi rabu da cin hanci da rashawa da dangoginsa.

Hani da aikata mummunan aiki: Hani da aikata mummuna, babu ko shakka cikamakin tabbatuwar umarni da aikata kyakkyawan aiki ne, domin kuwa a duk sa’ar da mutane suka dukufa wajen aikata kyakkyawan aiki to wannnan na nufin aikata mummuna aiki zai samu gagarumar koma-baya, in ma ba su yi adabo da shi ba. Ke nan duk inda ka ji umarni da aikata kyakkyawan aiki, to ka ji hani da mummunan aiki – Danjuma ne da Danjummai.

Duk mutumin da yake kokarin aikata kyakkyawan aiki kuma yake kokarin haramta wa kansa aikata mummunan aiki, to zai yi wuya ka same shi yana handame dukiyar da aka samar don gudanar da bukatun da suka shafi al’umma, ko ka same shi yana cusa kai cikin kowace irin almundahana. Ashe ke nan duk al’ummar da ta tsinci kanta tana aiwatarwa ko dabbaka wadannan ’yan tagwaye (umarni da aikata kyakkyawa da kuma hani da aikata mummuna), to babu shakka, babu ta yadda za a yi ta tsinci kanta tana aikata wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa.

Rashin ’yan tagwayen nan cikin al’ummarmu shi ya sa muka tsinci kanmu cikin halin da muke ciki. Musulunci kwata-kwata ya tsani duk wani sabo da kuma tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba. Annabin Rahama (SAW) ya umarci Musulmi da su nesanta daga azurta kansu ta hanyar haram, inda aka rawaito shi yana cewa: “Duk tsokar (jiki) da ta ginu ta hanyar cin haram, to ba ta da makoma (a gobe Kiyama) face wuta.”

A wani Hadisin kuma, Annabi Muhammad (SAW) ya nuna bacin ransa ga wani mai kula da karba da tattara Zakka da ya kawo Zakkar da ya karbo ya ware wasu kaya da mutanen suka ba shi kyauta, sai ya ce masa: “Wane hakki kake da shi har kake ware wasu kana cewa naka ne? Yanzu da ka zauna a gidan mahaifinka (ba mu sa ka aikin karbo Zakkar ba) shin za ka samu wadannan da kake cewa naka ne?”

Nan take Annabi ya umarce shi ya maido da abin da ya ware don ba hakkinsa ba ne. Wannan Hadisin na koya mana yin tsantseni da duk wani abin amfani da zai gifta ta ofishin da aka ba mu amanar gudanar da shi, ba kawai duk abin da ya zo mana ba mu rika kallonsa a matsayin ‘alherin ofis’ ba. Kullum Musulunci yana koya wa mabiyansa yadda za su mallaki zukatansu ta hanyar gintse soye-soyen zukatansu da ba sa kan hanya madaidaiciya. Sannan Hadisin yana kira ga duk wani Musulmi da ya tarbiyyantu da yin adalci da siffantuwa da halaye nagari da yin hannun-riga da duk wani mummunan aiki, don tabbatar da ci gaba mai dorewa a karan kansa da kuma al’umma gaba daya.

Yin imani da Allah da sakankancewa da cewa Shi ne Mahalicci Mai kaddarawa, Mai arzutawa, Mai talautawa, yana da muhimmanci a rayuwar dan Adam. Rashin imani da kin yarda da Allah cikin wadancan siffofin naSa, kamar yadda muke nunawa a aikace, shi yake jagora zuwa ga fadawa cikin wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa a kasar nan. Matukar ma’aikacin gwamnati ko ma duk wanda aka danka wa wata amana ta al’umma zai yi imani da Allah da sakankancewa da cewa Allahn nan dai Shi ne Mai azurtawa, kuma Mai talautawa – sakankancewa ta hakika, to ba ta yadda za a yi ka same shi yana handama da babakere kan abin da aka danka masa amana. Allah cikin LittafinSa Mai girma (K:65:2-3) Yana cewa:

“…kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, to (Allah) zai sanya masa mafita (a duk al’amuransa), Ya kuma azurta shi ta inda ba ya zato. Sannnan duk wanda ya dogara ga Allah (da sakankancewa a gare shi) to, Allah Ya isar masa….”

Hakika abin dubawa ne cewa a cikin wannan al’umma tamu, tsoron Allah ya yi karanci, in ma ba a ce babu shi kwata-kwata ba, a zukatanmu. Hakan kuwa ya hada da wadansu malaman addinan biyu (Musulunci da Kirista), wadanda a ka’ida su ne ya kamata su dasa mana tsoron Allah a zukatanmu ta hanyar wa’azozinsu. Soyayyar abin duniya da kyale-kyalen rayuwa, su suka yi katutu cikin zukatanmu. Mafi yawan mutane, muka zama bayi ga wannan duniya mai karewa, ta yadda muke ganin wadanda suka samu arzikin duniya da rayuwa mai kyau a matsayin wadanda Allah Ya yi wa gamo-da-katar, ba tare da yin tunani ta yaya suka tara wannan dukiya ba. To shi ke nan mu ma sai mu tsunduma tare da kudurcewa a rai, ko ta halin kaka sai mun tara irin wannan dukiya ta hanyar wa-ka-ci-ka-tashi da baitul malin kasa ta hanyar kowane irin nau’in cin hanci da rashawa da ya zo mana a rai.

Tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin mutane:

A Musulunci akan iya rusa tsarin cin hanci da rashawa ta hanyar tabbatar da adalci, wanda shi ne kashin bayan tabbatar kowace kasa da ke duniyar nan. Tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin mutane a Musulunci shi ne, da farko a dasa tsoron Allah a cikin zukatan mutane, sannan a samar da daidaito cikin raba arzikin kasa da kuma sama wa mutane ababen gudanar da rayuwarsu ta tilas da kuma kange masu karfi daga barin zaluntar marasa karfi, a cikin al’umma. Dabbaka wannan tsari yadda ya kamata a cikin al’umma ita ce hanya dodar ta fatattakar cin hanci da rashawa a cikin al’umma.