Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abeokuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara.
A bangaren dokoki kuwa, Sashi na 2 na Dokar ICPC (dokoki ne da aka samar don zakulowa da gabatar da ma’aikatan gwamnati masu cin hanci da rashawa a gaban kotu), ya fayyace cin hanci da rashawa da cewa, duk wani laifi da ya shafi karbar na-goro da sama-da-fadi da duk wasu laifuffuka masu jibi da wadannan, don samun wata fa’ida ga mai bayarwar, ko mai karbar. A dunkule dai, ka iya cewa cin hanci da rashawa shi ne: duk wani hali na nuna rashin gaskiya da kin bin ka’ida na mutumin da aka danka wa wata amana; ko aka ba shi wani matsayi ko shugabanci amma sai yake gudanar da su don amfanin kansa; ko na wadansu tsirarun mutane kawai. Gaba daya dai ta wadannan ma’anoni da muka bayar daga masana fannonin rayuwa daban-daban, za mu iya cewa lallai cin hanci da rashawa suna da alaka ta kut-da-kut da son tarawa ko samun abin duniya ta kowace hanya! Tunda haka ne kuwa, cikin ruwan sanyi za mu iya cewa cin hanci da rashawa a Musulunci, ya hada da duk wani rashin gaskiya da cin amana da rashin adalci da saba wa duk wata doka (da ba ta ci karo da ta Allah da ManzonSa ba), a gida ne ko a wajen aiki ne ko a makaranta, kai ko a filin wasa ne, dukkansu za su iya ishara zuwa ga cin hanci da rashawa. Domin duk mai aikata irin wadancan laifuffukan, yana yi ne don samun wata fa’ida ga karan-kansa. Shi kuwa Musulunci yana da ruwa-da-tsaki cikin gudanar rayuwar dan Adam dukkanta, don haka ne ma ya kalli matsalar cin hanci da rashawa ta fuska mai fadin gaske.
Rabe-raben cin hanci da rashawa:
Cin hanci da rashawa yakan zo ta fuskoki da ma’anoni daban-daban da mutane kan danganta shi da ita. Ta kai matsayin da a yau zai yi wuya mutum ya shiga wata hukuma ta gwamnati ko ta masu zaman kansu, ba tare da ya tarar da ana gudanar da wannan mummunar ta’ada ta salo da halaye iri-iri ba. Ba kawai a hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu ko a siyasa ake tafka wannan ta’asa ba, a’a, tana nan a ko’ina har a cikin gidajenmu da kasuwanninmu da sauransu. To, amma saboda mu kara fahimta da sake tantance wannan annoba ta cin hanci da rashawa, bari mu tattauna a takaice kan wasu manya kuma shahararru a fagen aikata wannan aika-aika da ta dade tana rusa al’ummar duniya, musamman ’yan Najeriya.
Cin hanci da rashawa a fagen siyasa:
An rubuta littattafai da dama, sannan masana daga fannoni daban-daban sun tattauna kuma a kullum kafofin watsa labarai ta sun tattauna ko suna kan tattaunawa a kan munin cin hanci da rashawa da ke faruwa a wannan fage na siyasa. Amma abin mamaki shi ne, su wadanda ake yi don su din (’yan siyasa), ko gezau ba su yi don yin wani abu na a-zo-a-gani wajen dakile wannan mummunar ta’ada a wannan fage. Kullum ji suke yi kamar sun fi karfin doka!
Shi cin hanci da rashawa a fagen siyasa yakan zo da fuskoki daban-daban, kamar yin almubazzaranci da ba da toshiyar baki da yin tsafe-tsafe da uwa-uba yin magudi a lokacin zabe da sauransu. Kai, in takaice muku, a duk nau’ukan da ake da su na cin hanci da rashawa a Najeriya, cin hanci da rashawa a fagen siyasa ya fi kowanne muni. Za ka samu a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, cin hanci da rashawa ya zama wani halattaccen abu. Za ka samu matasa da dattawa suna ta rige-rigen samun wata kujerar siyasa don kawai irin romo ko ‘alheri’ da ake samu idan an hau ta. Irin wadannan ’yan siyasa sun yi imani cewa da zarar sun dare irin wadannan mukamai na siyasa (duk kankantarsu kuwa), to shi ke nan kakarsu ta yanke saka, don za su yi amfani da wannan damar wajen cika lalitarsu da dukiyar al’umma.
Daka wasoso a kan dukiyar jama’a a Najeriya ya zama ruwan dare game duniya, irin wadannan shugabannin siyasa sun habaka tattalin arzikin kasashe da dama (a yayin da suka kashe nasu murus), ta hanyar wawashe kudaden kasarsu suke kai ajiya a bankunan wadancan kasashe. Bayanai da kididdiga masu tushe sun tabbatar da cewa mahukuntan Najeriya suke sahun gaba wajen tabarbarar da tattalin arzikin kasar, ta hanyar nuna kuruciyar bera sannan su jibge abin da suka sace a bankunan kasashen waje.
Wani nau’in na cin hanci da rashawa da ke faruwa a wannan fage na siyasa shi ne tsafe-tsafe, musamman da kananan yara. A duk lokacin da aka ce an kada kugen siyasa, akan samu yawaitar batar kananan yara a wasu wurare da dama a Najeriya. Wadannan yara da ake ba da rahoton batarsu a irin wannan lokaci, bayanai sun tabbatar da cewa ana amfani da su ne wajen aikata tsafe-tsafe don cimma burin samun wata dama ta musamman don kai wa ga lashe zabe. Wannan ma cin hanci da rashawa ne (kin gaskiya da rashin bin ka’ida) kuma ya hada da rashin imani, (saboda ya jawo raba dan Adam da ransa) don cin zabe.
Sai kuma ta fuskar magudi: Yin magudi a yayin zabe ya zama ruwan dare game duniya. A mafi yawan lokuta, mafi yawan ’yan takara a kowane matakin zabe sukan bi kowace irin hanya don kaiwa ga cin zabe. A lokacin zaben za ka samu ’yan takara kan yi hayar matasa zauna-gari-banza, wadanda za su yi amfani da su a tashoshin kada kuri’a don sace akwatuna da katunan zabe (a inda suka ga ba su da rinjaye), don cika su da dangwalallun takardun zabe na dan siyasar da ya dauki hayarsu ya kai gaci, kodayake sabuwar dabarar yin hakan a ’yan shekarun nan, ita ce ta saye takardun zaben daga wajen jami’an zabe don aikata wannan rashin gaskiya.
Cin hanci da rashawa a jami’o’i da manyan makarantunmu:
Ba wani sabon abu ba ne ga dan Najariya yadda cin hanci da rashawa ya zama wani abin ado a jami’o’inmu da kwalejojin iliminmu ba. Malaman irin wadannan makarantu kan yi amfani da damarsu wajen tursasa dalibai mata don yin lalata da su. Bayan wadannan dalibai mata sun ba da kansu ga irin wadancan malamai, to shi ke nan, su kuma malaman sai su daga darajar sakamakon jarrabawar wadannan dalibai, wadanda ko kadan ba su cancanci wannan darajar ba a zahiri. Wani lokaci mutum kan tambayi kansa, ta yaya wadansu daliban suke samun kansu a matsayin dalibai a jami’a? Tabbas wadansu sun shiga jami’ar ce bisa cancanta, to amma wadansu sun shigo ta ce ta hanyar da ba ta dace ba. Wannan ya faru sau da yawa daga daliban da suka cancanci shiga jami’ar saboda cika ka’idojin shigar, ba su samun shiga.