✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakamata a dakatar da gasar cin kofin Afirka a wannan karo -Enyeama

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuma golan Najeriya bincent Enyeama ya yi kira ga Hukumar Shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta…

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuma golan Najeriya bincent Enyeama ya yi kira ga Hukumar Shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta dage gasar cin kofin Afirka da zai gudana a Maroko a badi saboda matsalar yaduwar cutar Ebola.

Enyeama wanda yanzu haka yake kwallo a kulob din Lille da ke Faransa, ya ce dalilin da ya sa ya bayar da wannan shwarara ga hukumar don ta dage gasar a badi shi ne ganin yadda cutar ebola take yaduwa musamman a kasashen Afirka ta yamma da wasu yankunan Afirka.
dan kimanin shekara 32 ya ce idan aka yi la’akari da yadda cutar ta kashe akalla mutum dubu 5 kawo yanzu akwai yiwuwar cutar za ta cigaba da yaduwa a lokacin gasar musamman ganin gasa ce da za ta hada sassa daban-daban na Afirka.
dan kwallon ya ce gaskiya akwai hatsari a yi gasar a wannan lokaci da cutar ebola ta yi wa Afirka katutu don haka nake ba hukumar shawarar ta dage gasar zuwa wani lokaci bayan an shawo kanta.
“Cutar za ta iya cigaba da yaduwa musamman ganin ana harbuwa da ita ne ta hanyoyin runguma da yin musabaha da sauransu kuma babu yadda za a yi a tara dubban jama’a a gasar ba tare da an yi wadannan abubuwa da na lissafa ba”, inji shi.