✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU: Hana malaman jami’a albashi ba laifi ba ne

Lauyoyi sun ce matakin da gwamanti ta dauka na kin biyan albashin lakcarori masu yajin aiki bai saba doka ba

Lauyoyi sun bayyana cewa matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na kin biyan albashin malaman jami’a da ke yakin aiki bai saba doka ba.

Lauyoyin sun bayyana haka ne bayan Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa gwamnat ba za ta biya albashin malaman jami’a na wata shida da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta shafe wata shida tana yi ba.

Ministan ya bayyana haka ne a zaman da suka tashi baram-baram da ASUU, inda ya bayyana musu cewa sun rasa albashin watannin da suka yi suna yajin aiki.

A martaninsa, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce idan gwamnati ba ta biya su albashin ba, ba za su tantance rukuni biyu na daliban da ke jiran fara karatu a jami’o’i ba.

Amma a tsokacin wasu lauyoyi kan matakin wasu lauyoyi sun bayyana cewa tsarin gwamnati na babu-aiki, babu-biya bai saba doka ba, saboda ya dace da Dokar Kungiyoyin Kwadago ta 2005.

Sashe na 43(1) (a) ya ce: “Duk ma’aikacin da ya shiga yajin aiki zai rasa albashi da sauran hakkoki na tsawon lokacin yajin aikin, ba za a lissafa yajin aikin a shekarun aikinsa ba, kazalika duk wasu hakkoki da suka danganci lokacin aiki hakan zai shafe su.” 

Wani lauya, Yusuf Buhari, ya ce ko da babu dokar, a kowane dole akwai sharudda da ka’idoji.   

“Idan ka yi yajin aikin to ya kamata a wanda kake wa aiki ya samu hakkin rike albashi. Irin wannan yarjeniya ba ta haramta ba,” in ji shi. 

Shi ma wani lauya, Hamid Ajibola Jimoh ya bayyana cewa sashe na 43(1)(a) da kuma (b) na Dokar Kungiyar Kwadago ba ta haramta yajin aiki ba, amma ta bayyana cewa ba za a biya ma’aikacin da ya yi yajin aiki albashi ba.   

Shi ma, E.M.D. Umukoro ya ce har yanzu Dokar Kungiyar Kwadag na nan tana aiki, sai dai, “idan an yi mata kwaskwarima ko kuma kuto ta soke ta.