Gwamnatin Tarayya ta umarci Shugabannin jami’o’in Najeriya da su gaggauta sake bude makarantunsu don dalibai su ci gaba da karatunsu.
Umarnin na kunshe ne a cikin wata wasika da Daraktan Kudi na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Sam Onazi, ya fitar a madadin shugaban NUC, Farfesa Abubakar Rasheed ranar Litinin.
- Hango jiragen soji ya sa ’yan ISWAP guduwa su bar mutanen da suka sace a Borno
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 22 a Birnin Gwari
Jaridar Punch ta rawaito cewa wasikar wacce aka aike wa dukkan shugabannin makarantun Gwamnatin Tarayya da iyayen jami’o’in da ma hukumomin gudanarwarsu ta ce ya zama dole a sake bude makarantun.
“Ku tabbatar mambobin ASUU sun dawo kuma sun fara gudanar da lakca tare da dawo da harkokin yau da kullum a cikin jami’o’in,” kamar yadda wani bangare na wasikar yake cewa.
A ranar Larabar da ta gabata ce dai Kotun Ma’aikata ta umarci Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta janye yajin aikinta, kodayake daga bisani kungiyar ta daukaka kara.
Tun a watan Fabrairun wannan shekarar ne dai malaman jami’o’in suka tsunduma yajin aikin tare da shan alwashin cewa ba za su koma ba har sai gwamnati ta cika musu alkawuransu.