Shugaban Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman gurbin karatu a manyan makarantu ta Najeriya, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce yajin aikin da mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke gudanarwa a halin yanzu ba shi da wata fa’ida.
Farfesa Oloyede ya bayyana hakan ne a yayin da yake mika wasu muhimman injina da na’urorin kula da lafiya na biliyoyin naira ga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) don inganta ayyukan kiwon lafiya a Najeriya.
- Kannywood za ta iya gogayya da takwarorinta na duniya —Rukky Alim
- An yi wa maniyyatan Kano bitar Aikin Hajji a aikace
Oloyede ya mika na’urorin ne a madadin wata babbar hukuma ta kasar Amurka da ta assasa wani shiri na inganta ayyukan kiwon lafiya da ta yi wa lakabi da Project Cure.
A cewarsa, yajin aikin kungiyar ASUU da ya ki ci ya ki cinyewa kuma wanda ake fama da shi a manyan makarantun kasar na iya haifar da mummunar barna ga dalibai da harkokin ilimi da ba za a iya magance ta ba a kasar.
Ya ce, “duk da na yarda cewa samar da kudaden gudanarwa (ko dan kaka) ga cibiyoyin lafiya da kuma makarantu babban nauyi ne da ya rataya a wuyan Gwamnati, ina kuma kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi la’akari da girman barnar da wannan yajin aiki a kai-a kai ke haifarwa ba iya ga dalibai ga kadai ba har ma da kasa baki daya.”
Farfesa Adesoye ya ce rawar da Hukumar JAMB take takawa a fagen harkokin kiwon lafiya tana tallafa wa kokarin da Gwamnati ke yi wajen cike gibin da ake da shi a kasar nan musamman a fannin gine-gine a cibiyoyin kula da lafiya.
Ya ce JAMB za ta ci gaba tattali da kuma ririta kudaden da take kashewa, domin samun rarar da za ta tallafa wa manyan cibiyoyin kiwon lafiya da kuma makarantu a fadin kasar nan.
Sauran cibiyoyin kiwon lafiya da suka ribaci wannan tallafi sun hada da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maduguri, Asibitin koyarwa na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano da karin wasu cibiyoyin 9 daga sassa shida na kasar nan.