Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU, ta fara shirin sake fadawa wani sabon yajin aikin a yayin da gwamnatin Tarayya ta gaza biyan albashin watannin 13 na mambobinta fiye da dubu daya a fadin kasar.
Shugaban ASUU reshen Jami’ar Jos, Dokta Lazarus Maigoro ne ya yi barazana hakan a ranar Lahadi, inda ya yi gargadin cewa gwamnatin Tarayya ta rike wasu alawus na mambobinta.
- ’Yan bindiga 15 sun kwanta dama yayin artabu da sojoji a Neja
- NDLEA ta cafke jami’in tsaro da hodar iblis a Ogun
Dokta Maigoro ya zargi Babban Akanta na Kasa, Ahmed Idris, da hana malaman albashinsu duk da cewa na cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da kungiyar dangane da biyan albashin da suka biyo, lamarin da ya sanya suka janye yajin aikin da suka yi na baya-bayan nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Dokta Maigoro ya yi zargin ana yi wa malaman barazanar cewa ko dai su bari a saka su cikin tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS, ko kuma a ci gaba da rike albashin nasu.
“Galibin abokan aikinmu a Jami’ar Jos ba a biya su albashi ba tun daga watan Fabrairun 2020, saboda haka ta ya ake tunanin za su rika zuwa wurin aiki.
“Muna fatan a yanzu duk wani mataki da kungiyar ta dauka ’yan Najeriya ba za su kalle shi da wata manufar ba, musamman ganin yadda gwamnati da mutanen gari suka yi shiru game da rashin tabbatar da yarjejeniyar da muka kulla tun a shekarar 2020,” a cewarsa.
Ana iya tuna cewa, yajin aikin baya bayan da ASUU ta yi daliba sun shafe fiye da watanni tara suna zaman dirshen a gida ba tare da zuwa makaranta ba.