Ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu, ya gayyaci wakilan Kungiyar Malaman Jami’o’in kasar (ASUU) zuwa taron gaggawa, bayan barazanar sake shiga wani yajin aiki da kungiyar ta yi.
Za a gudanar da taron na gaggawa da misalin karfe 11.00 na safiyar Talata, 6 ga watan Afrilun, 2021.
- Dalibai biyar na Kwalejin Harkokin Noma ta Kaduna sun kubuta
- Bishop Kukah ya caccaki Buhari kan matsalar tsaro
Sanarwar da Daraktan Yada Labarain Ma’aikatar Ilimi, Ben Bem Goong ya fitar, ta ce za a gudanar da taron ne a Hedikwatar Ma’aikatar da ke birnin Abuja.
Yayin bayyana dalilinsa, Ministan ya ce an kira taron na gaggawa ne domin dinke barakar da ke iya kaiwa ga malaman jami’ar su shiga yajin aikin da suke shirin yi.
ASUU ta yi barazanar sake komawa yajin aikin da ta dakatar ne saboda abun da ta kira cin zarafin da ake yi wa mambobinta da kuma kin biyan su albashinsu na tsawon wata 10.
Ana iya tuna cewa, a watan Janairun da ya gabata ne ASUU ta janye yajin aikinta na wata tara bayan daidaitawa da Gwamnatin kan wata muhimmiyar yarjejeniya da ta shafin bukatun malaman.