Wakilan Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago na ganawar sirri domin shawo kan kungiyoyin su jingine shirinsu na shiga yajin aikin kyamar karin farashin man fatur da wutar lantarki.
Gabanin fara zaman Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bukaci kungiyoyin su jingine batun shiga yakin aikin da suke son farawa.
A martaninsa, Shugaban Kungiyar Gamayyar Ma’aikata (TUC) Quadri Olaleye, ya ce idan har da gaske gwamnati take yi, to kamata ya yi tuntubi ‘yan kwadago kafin a yi karin farashin.
Taron wanda Ministan Kwadago, Chris Ngige ke jagoranta na gudanan ne a dakin taro na Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa.
Sauran wakilan Gwamantin Tarayya da ke halartar zaman sun hada da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed; Minista a Ma’akatar Kwadago, Festus Keyamo; Ministan Lantarki, Saleh Mamman; da kuma Minista a Ma’akatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva.
Bangaren ‘yan kwadago ya samu halarcin Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Ayuba Wabba da takwaransa na TUC, Quadri Olaleye.