Gwamnatin Najeriya ta umarci manyan lokitoci a Asibitocin Koyarwa da ke fadin kasar su bude kundin rajista da zai ke ba da bayanai kan likitoci da ke yajin aiki a wani mataki na daina biyan su albashi.
Wani babban jami’in kiwon lafiya ne ya shaida da hakan ga manema labarai, inda Dokta Uyilawa Okhuaihesuyi, Shugaban Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD ya tabbatar a ranar Lahadi.
Sanarwar da Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya fitar ta ce daga gobe Talata dokar ‘ba-aiki ba-albashi’ za ta soma aiki kan duk wani likita da ya amsa kiran kungiyar likitoci masu neman kwarewa na shiga yajin aiki.
Wannan dambarwa tsakanin gwamnati da likitoci na haifar da barazana ga marasa lafiya a asibitoci kasar inda tun a makon da ya gabata mutane ke ta kwashe ’yan uwansu da ke jinya daga asibitoci saboda rashin samun kulawa.
A Litinin din makon da ya gabata likitocin suka koma yajin aiki da suka dakatar a ranar 10 ga watan Afrilu bayan alkawarin da gwamnati ta yi musu na biya musu bukatunsu, ciki har da biyansu wasu kudade da alawus-alawus.
Sai dai a cewar likitocin bayan cike kwana 100 da wadannan alkawura gwamnati ta gagara biya musu bukatunsu, dalilan da suka tunzura su sake komawa yajin aiki.
Dokta Okhuaihesuyi ya ce ba su razana da barazanar gwamnati ba domin babu yada za a yi gwamnati ta iya maye gurbin likitoci 16,000 da sabbi.