Gwamantin Tarayya ta gayyaci shugabannin Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) domin tattaunawa bayan sun fara yajin aiki.
Gwamnatin ta bukaci a yin zaman ne a ranar Alhamis, a yayin da marasa lafiya ke ta gunaguni bayan yajin aikin ya sa likitocin sun yi watsi da su tun ranar Litinin.
Likitocin sun tsunduma yajin aikin ne saboda gwamnatin ta gaza cika wasu alkawuran da ta yi musu a baya.
Ministan Kwadago, Chris Ngige ya bayyana mamakinsa game da shiga yajin aikin da likitocin suka yi, bayan zaman da ya ce ya yi da shugabanninsu a makon jiya, sun kuma fahimci juna.
A ranar Laraba, kakakin Ma’aikatar, Charles Akpan, ya ce zaman da aka dage daga ranar Laraba zuwa Alhamis zai gudana ne a dakin taro da ke hedikwatar ma’aikatar da misalin karfe 2 na rana.