Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya nemi Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da takwararta ta TUC da su kalli matsalolin da ‘yan Najeriya za su fada idan suka tsunduma yajin aiki.
Gbajabiamila na yin kiran ne a dadai lokacin da shugabannin kungiyoyi, Ayuba Wabba da Quadri Olaleye, suka amsa gayyatar da ya yi musu domin a sasanta yunkurin shiga yajin aiki da su ke yi a ranar Latinin.
Matukar dai ba a sami maslaha tsakanin gwamnati da ‘yan kwadagon ba, to da safiyar Litinin, 28 ga watan Satumbar 2020 ne za su tsunduma yajin aikin.
A bayanin bude taron, Gbajabiamila da shgabannin kwadagon sun nuna rashin jin dadinsu kan karin kudaden man fetur da na wutar lantarki da gwamnati ta yi a kwanan nan.
“Mu da ke nan majalisar muna tare da ku akan hakan,” inji Gbajabiamila
Ya kuma gargadi gamayyar kungiyoyin kwadagon da su yi la’akari da matsalolin da mutane za su shiga sakamakon kulle ma’aikatun gwamnatin lokacin yajin aikin, tare da yin kira kan su janye yunkurin nasu na shiga yajin aikin.
Idan dai za a iya tuanwa, kokarin sassancin da ake yi tsakanin kungiyoyin da gwamnatin tarayya kan karin kudin man fetur da wutar lantarki na neman ya ci tura wanda har ya kai kungiyoyin na neman daukar matakin da nufin tilasta gwamnatin ta janye karin.
Ko a makon da ya gabata sai da wata kotun ma’aikata ta haramtawa gamayyar kungiyoyin kwadagon shiga yajin aiki, amma su ka yi fatali da hukuncin, su na masu cewar janye karin ne kadai zai hana su shiga.
Olaleye ya jinjina wa kakakin majalisar kan yadda ya ke ruwa da tsaki wajen ganin an magance duk wasu matsaloli tsakaninsu da gwamnatin tarayya.