A halin yanzu Shugaban dunkulalliyar kungiyar dillalan shanu da kayan abinci ta kasa AUFCDN, Muhammad Tahir yana hannun hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.
Sakataren AUFCDN, Ahmed Alaramma ne bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai ranar Litinin a hedikwatar kungiyar kwadago NLC da ke Abuja.
- An samu masu bautar marakin da aka haifa da kai biyu
- Mukabala: Sheik Abduljabbar ya amsa gayyata, ya gindaya sharudda
- Yajin aiki: Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabo a Kudu
Alaramma ya ce jami’an tsaro na yunkurin tunzura mambobin kungiyarsu wanda ya kamata gwamnatin tarayya ta farga wajen yin ruwa da tsaki domin ganin tarzoma bata kunno kai a kasar ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, kungiyar AUFCDN wadda wani bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa, ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Alhamis bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ta bai wa gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta.
Kungiyar ta lashin takobin cewa yajin aikin zai ci gaba da dorewa musamman wajen ganin ta dakile isar kayan abinci da dabbobi zuwa Kudancin Najeriya.
A kan hukuncin da kungiyar ta yanke, tana son gwamnati ta bai wa mambobinta kariya tare da biyanta diyyar naira biliyan 475 kan kisan da aka yi wa ’ya’yanta da kuma asarar da ta tafke a yayin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.