Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU) ta bai wa gwamnatin kasar wa’adin mako uku ta cika alkawarin da ta yi na biyan wasu bukatun ’ya’yanta ko kuma su shiga yajin aiki.
Kungiyar ta yanke shawarar bai wa gwamnati wa’adin ne a wani taron Majalisar Kolinta da ta gudanar ranar Litinin a Abuja.
- Daily Trust na kiran masu harkar noma su ci gajiyar shafin TrustPlus
- Gumi ya bude wa makiyaya makaranta a Kaduna
Kungiyar ASUU ta bayyana cewa ta yanke shawarar bai wa gwamnati mako uku ne ko ta cika alkawarin da ta yi wa ’ya’yanta yau tsawon shekara.
ASUU ta ce muddin ba haka ba za ta umurci ’ya’yanta da su shiga yajin aiki na sai abin da hali ya yi, saboda sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.
Shugaban kungiyar na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya jagoranci zaman ya ce ba su da zabi face ba da wa’adin.
Farfesa Osodeke ya ce wajibi ne gwamnatin ta cika masu alkawarran da su ka sanya wa hannu yayin zaman da suka da ita tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.