Kasar Isra’ila ta raba wa al’ummar Fulani tallafin kayan abinci don su yi yin bikin Karamar Sallah a Abuja.
Shirin jin kai na al’ummar Yahudawa na ChabadAid da hadin gwiwar Ofishin Jakadancin Isra’ila na Najeriya ne suka raba kayan ranar Laraba.
- Sojoji sun cafke shugaban kungiyar IPOB
- Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi
- Yadda gobarar gas ta kashe ’yan gida daya
Kayan da aka raba wa Fulanin sun hada da shinkafa, wake, man girki, taliya da masara a Ruga Jadi, Ruga Sauka da kauyukan Ruga Besa da sauransu.
Limamin al’ummar Yahudawa a Najeriya, Rabbi Israel Uzan, wanda ya gabatar da kayayyakin abincin, ya ce manufarsu ita ce isa ga duk al’ummomin Musulmin Najeriya.
Ya ce kodayake Yahudawa na fuskantar kalubale a duniya, tallafin zai inganta zaman tare tsakaninsu da Musulman Najeriya, a matsayin misali ga duk duniya.
“Za mu yi kokarin taimakawa inda za mu iya bayar da irin wannan a halin yanzu, muna kuma aiki tare da wasu kungiyoyin Musulmai kuma sun tura mu zuwa inda akwai manyan bukatu na yau da kullun.
“Tabbas, za mu ci gaba da aiwatar da irin wadannan ayyukan kuma a nan gaba gudunmawar tamu za ta karu, inda za mu iya zayayawa Najeriya gaba daya.
“Mun mayar da hankali kan ci gaban mutane, ilimi, ayyukan kiwon lafiya da samar da ruwan sha; don haka mun fi mayar da hankali kan bunkasa dan Adam a wannan lokaci na COVID-19 da Ramadan.
“Ana bukatar abinci shi ya sa muka ba da kayan abincin, mun kuma tattauna da wasu abokanmu Yahudawa kan samar da makaranta a cikin al’umma.
“Mun kafa tsarin samar da ruwa, nan da ’yan watanni za mu yi kokarin kafa makarantu tare da duk tsarin karatun da za su bukata,” kamar yadda ya bayyana.
Da yake karbar kayayyakin a madadin al’ummar Fulani, Bature Adamu ya nuna jin dadinsa ga Isra’ila da ChabadAid game da gudummawar.
“Al’umma sun yi farin ciki da gudummawar da rijiyoyin da suka samar mana.
“Al’ummarmu suna bukatar makarantu da Masallatai, duk da cewa ba mu da su tukunna, sun yi alkawarin gina mana su.
“A yanzu sun kawo abinci sun samar da rijiyar burtsatse, ba mu da asibiti amma mu shiga gari don samun damar kula da lafiya,” inji shi.