Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya nada Ohi na Okenwe, Alhaji Ahmed Tijani Anaje, a matsayin sabon Ohinoyi na kasar Ebira ranar Litinin.
Gwamnan ya tube rawanin wasu manyan sarakunan yanka ya kore su daga jihar, sannan ya nada wasu sabbin sarakunan gargajiya.
Sabon Ohinoyi, Alhaji Ahmed Tijani Anaje ya zama magazin Ohinoyi AbdulRahaman Ado Ibrahim, wanda ya rasu a ranar 29 ga Oktoba, 2023.
Gwamnan ya ce Ahmed Tijani Anaje da sauran sabbin sarakunan, za su cike gibin da aka samu a sarautun, bayan gwamnatin jihar ta warware takaddamar da ta kunno kai wajen zaben su.
- Kisan Nafi’u: Kotu ta dage Shari’ar Hafsat Chuchu
- Kotu ta umarci Gwamnati ta biya Emefiele diyyar N100m
Fitattun mutane 71 ’yan kabilar Ebira suka tsaya takarar kujerar Ohinnoyi, wadda a karshe bayan tantance su aka ba gwamnatin jihar shawara nada Ohi na Okenwe a kan kujerar.
A wani zama da suka yi ranar Asabar a gidan gwamnati, Gwamna Bello ya bukaci masu neman kujerar da su mara wa duk wanda ya yi nasara cikinsu baya.
Nadin Sabbin Sarakuna
Yahaya Bello ya nada Alhaji Ibrahim Gambo Kabir a matsayin Maigarin Lokoja, sakamakon rasuwar Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi III a ranar 29 ga Satumba, 2022.
Haka kuma ya nada Alhaji Dauda Isah a matsayin Maiyaki na yankin Kupa da ke Karamar Hukumar Lokoja.
Sallamar Sarakunan Yanka
A gefe guda kuma gwamnan ya tube rawanin wasu sarakuna uku masu daraja ta daya, ciki har da Ohimege-Igu na Koton-Karfe, daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar.
Ya ce matakin nasa ya biyo bayan korafe-korafe kan sarakunan da abin ya shafa ne, da kuma saba dokokin sarauta da sauran dokoki da suka yi.
Yahaya Bello ya ce: “An tube rawanin Ohimege-Igu na Koton-Karfe, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Gargajiya ta Karamar Hukumar Lokoja/Kogi, Alhaji Abdulrazaq Isah Koto, wanda yanzu zai koma da Karamar Hukumar Rijau a Jihar Neja da zama.
“Majalisar Masarauta Odaki a Karamar Hukumar Lokoja/Kogi ta amince da nadin Mallam Saidu Akawo Salihu a matsayin Ohimege-Igu na Koton-Karfe, kuma za a yi masa nadi ba tare da bata lokaci ba don kauce wa samun gibi,” in ji shi.
“An tube Olu Magongo na Magongo, Sam Bola Ojoa, wanda zai koma da zama garin Salka na Karamar Hukumar Magama ta Jihar Neja.
“An kuma tsige Obobanyi na Emani, Samuel Adayi Onimisi, wanda za a kai shi garin Doko, Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja.
Dakatarwa
Sanarwar ta kara da cewa, “Mai martaba, Boniface Musa, ONU-IFE a karamar hukumar Omala za a dakatar da shi har abada.”
A watannin baya an ba wa sarakunan gargajiyar da abin ya shafa takardar horo kan wasu batutuwa da suka danganci da tashe-tashen hankula da dangoginsu a yankunansu.
Gwamnan ya kuma mayar da sunan Obaniyi na Ihimi zuwa ga Obobanyi na Emani, yana mai cewa “batun sunan sarautar na gaban kotu kuma har yanzu kotun ba ta kai ga yanke hukuncin karshe ba”.