Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a kan Naira miliyan 500 a shari’ar zargin sa da karkatar da Naira biliyan 80.
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙi (EFCC) ce ta gurfanar da Yahaya Bello kan zargin karkatar da kuɗaɗen a lokacin da yake gwamna.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da belin da sharadin tsohon gwamnan zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa, kowannensu zai ajiye kwatankwacin wannan kuɗi.
Wajibi ne kowannensu ya mallaki gida a Abuja sannan ya sako wa kotu takardun gidajen domin ta tantance.