Ubangiji Allah Mai jinkai ne, Mai tausayi da hakuri, Yana so ganin cewa mu ma mun bi irin naSa gurbin. Ka duba dai cikin duniyar nan da muke raye yau, abubuwa da dama suna faruwa na ban tsoro da mamaki, mugunta da rashin kauna sai yawaita suke yi. Ba haka Ubangiji Yake so mu zamo ba, Ya ba mu ’yanci cikin rayuwarmu don kaunarSa gare mu, amma sai muka dauki wannan ’yancin ba komai ba, mun fi son bin namu nufi fiye da na Ubangiji Allah
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka, Mai kauna, Mai alheri.
Barkanmu da sake haduwa a wannan mako inda za mu yi nazari a kan yafe wa juna.
Da dama mukan ji mutane suna cewa “Ba zan taba yafe masa ko mata ba har duniya ta tashi” Wai! Anya kuwa? Wane irin laifi ne wannan da mutum ba zai iya yafewa ba har duniya ta tashi? Sannan kana iya rokon gafara wurin Ubangiji Allah Ya yafe maka laifin da ka yi? Babu shakka a zamanmu na nama da jini mukan iya saba wa juna a fanoni daban-daban cikin harkokinmu na yau da kullum, to sai a ce dukanmu ba ma iya yafe wa juna, a ganinka yaya duniyar za ta zamo a yau? Wani laifin na da zafi kwarai da gaske, har ma yakan bar gurbi da a duk lokacin da ka gani sai ka tuna, amma duk da haka bai kamata mu ki yafe wa juna ba, domin Ubangiji Allah na fadi cikin maganarSa cewa mu yafe wa juna don Shi ma Ya yafe mana. Alal misali, a ce duk laifin da muke yi wa Ubangiji Allah ba Ya yafe mana, a ganinka akwai wanda zai tsira? Babu. Bari mu ji abin da Littafi Mai tsarki ke fadi a nan: “Akwai wani Allah kamarKa, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gadonsa? Ba ya rikon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.” Mika:7:18. Ubangiji Allah Mai jinkai ne, Mai tausayi da hakuri, Yana so ganin cewa mu ma mun bi irin naSa gurbin. Ka duba dai cikin duniyar nan da muke raye yau, abubuwa da dama suna faruwa na ban tsoro da mamaki, mugunta da rashin kauna sai yawaita suke yi. Ba haka Ubangiji Yake so mu zamo ba, Ya ba mu ’yanci cikin rayuwarmu don kaunarSa gare mu, amma sai muka dauki wannan ’yancin ba komai ba, mun fi son bin namu nufi fiye da na Ubangiji Allah.
Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah Ya yafe muku ta wurin Almasihu. Afisawa 4:32
Ba da sauki yake ba a ce ka yafe wa wanda ya kashe maka ’ya ko danka ko mahaifi ko mahaifiyarka, ko kuma wani na kusa da kai. Rashin yafe wa wannan mai laifin ba zai dawo da su ba, shi ya sa idan ka san cewa Ubangiji Allah na da iko bisa komai, sai ka bar komai a hannunSa, ka kuma yafe wa wanda ya yi maka laifi. Ya rage tsakaninsa da Ubangiji domin Ubangiji zai shar’anta kowa da kowa bisa ga sakamakon abin da mutum ya yi a duniya. Shi ya sa Ubangiji na cewa mu nemi fuskarSa cikin addu’a mu bar mugayen ayyukanmu, mu nemi gafara daga wurinSa, Shi kuwa zai gafarta mana zunubanmu. “In jama’aTa wadanda ake kiransu da sunaNa za su yi tawali’u, su yi addu’a, su nemi fuskaTa, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa’an nan sai in ji su daga sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da kasarsu.” – Tarihi 7:14.
Har ma cikin Ikilisiya a yau, muna bukatar yafe wa juna kamar yadda Manzo Bulus ya gargadi masu bi cewa ta wurin yafewa ne za mu iya kawo masu yi mana laifi ga sanin Ubangiji da kaunarSa. “Amma in wani ya jawo bakin ciki, ba ni kadai ya jawo wa ba, amma ga wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawowa, ba tsanantawa nake yi ba. Irin mutumin nan, horon nan da galibin jama’a suka yi masa, ai, ya isa haka. Gara dai ku yafe masa, ku kuma karfafa masa zuciya, don kada gayar bakin ciki ya sha kansa. Saboda haka, ina rokonku ku tabbatar masa da kaunarku.” – 2 Korintiyawa 2:5-8
Bari mu ga wasu ayoyi da za su kara ba mu ganewa cikin nazarinmu:
Domin in kun yafe wa mutane laifufffukansu, Ubanku na sama zai yafe muku. In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba. – Matiyu 6:14-15
Saboda haka, sai ku dauki halin tausayi da kirki da tawali’u da salihanci da hakuri, idan ku zababbu ne na Allah, tsarkaka, kaunatattu, kuna jure wa juna, in kuma wani yana da kara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji Ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe. – Kolosiyawa 3:12-13
Ku rabu da kowane irin dacin rai da hassala da fushi da tankiya da yanke da kowane irin keta. Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah Ya yafe muku ta wurin Almasihu – Afisawa 4:31-32
Bari mugaye su bar irin al’amuransu, Su sake irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi Mai jinkai ne, Mai saurin gafartawa. – Ishaya 55:7
kauna tana sa hakuri da kirki. kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko. kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. – 1 Korintiyawa 13:4-6.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Ubangiji Allah Ya bar mu cikin masu rai.
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ganewa don mu zama da zuciyar yafe wa juna a koyaushe, amin.