✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ziyarar Shugaban Koriya ta Arewa ta kaya a birnin Beijing

Bayan kasashen Koriya ta Arewa da China sun dauki kwanaki ba tare da cewa uffan ba a kan ziyarar da Shugaban kasar Koriya ta Arewa…

Bayan kasashen Koriya ta Arewa da China sun dauki kwanaki ba tare da cewa uffan ba a kan ziyarar da Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya kai zuwa China, kasar China ta fitar da sanarwa a karon farko.

Gwamnatin China ta bar duniya a duhu na tsawon kwanaki duk da cewa ta san ana ta jiran samun tabbacin cewa Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ziyarci Beijing a karon farko, a wata ziyara mai matukar muhimmancin da ake tunanin zai kawo zaman lafiya a yankin.

Kamfanin Dillancin Labara na China ya fitar da bayanai kan ziyara ta farko mai tarihi, ta Shugaba Kim Jon-un tun da ya hau mulki shekara bakwai da suka wuce kamar yadda BBC ta ruwaito.

An ce a yayin ganawar, Shugaba di Jinping ya gaya wa takwaransa na Koriya ta Arewa  cewa China na nan kai-da-fata kan shirin raba yankin Koriya da makaman kare dangi.

A nasa bangaren Kim Jong-un ya ce watsi da shirin mallakar makaman kare dangi matsaya ce da Koriya ta Arewa ta yi amanna da ita.

Ana ganin wadannan kalamai alamu ne na Koriya ta Arewa na neman wata dama da za ta yi watsi da shirin nata na kera makaman  kare dangi salin-alin.

Tsohon mai shiga tsakani na Amurka a kan shirin mallakar makaman nukuliya na Koriya ta Arewa Christopher Hill, ya ce wannan ganawa tsakanin Shugaban Koriya ta Arewa da na China tana da matukar muhimmanci.

Ya ce: ‘’Hukumomin China sun nuna wa Kim Jon-un karara cewa ba za su karbe shi ba har sai ya koma kan turbar niyyar watsi da shirinsa na kera makaman nukuliya.’’ Kamar yadda BBC ta ruwaito.

Christopher Hill ya ce a yanzu dai China tana fatan cewa Shugaban na Koriya ta Arewa zai gabatar da batun watsi da makaman nukiliyar idan ya gana da Donald Trump.

Ziyarar ta Kim Jong-un a China kamar wata sharar fage ce ga ganawar da zai yi da Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in da kuma Shugaba Donald Trump na Amurka.