Mazauna unguwannin Shagari Kwatas da Maidile sun koka kan yadda matsalar zaizayar kasa ke barazana ga muhallansu.
Mazaunan sun ce wata katuwar kwata da ta taso daga rukunin masana’antu ta Sharada ta biyo ta Sabuwar Gandu ba wai kawai zaizaye kasar take yi ba, tana ma jawo babbar barazana ga yankunan Maidile, Shagari Kwatas da Sheka Dandaji.
“Wannan matsalar ta dade a unguwar nan, ko a kwanan nan sai da wasu gidaje biyu suka rushe sakamakon zaizayar da ruwa ke yi wa kasar wurin”, inji Aminu Babba, wani mazaunin Shagari Kwatas.
Ya koka cewa dagwalon da yake fitowa daga wasu masana’antun fata daga Sharada ya bi ta cikin kwatar na takura musu sosai ta yadda wata ran ko barci ba su iya yi.
To sai dai Aminiya ta lura cewa su ma jama’ar yankunan na ba da tasu gudunmawar ta hanyar jibge shara a cikin kwatar, wanda ke taimakawa wajen kara tabarbarewar lamarin.
Aminu ya ce, “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su kawo mana dauki kan matsalar. Kai a zahirin gaskiya ma akwai wani karamin daji da miyagu ke amfani da shi wajen shaye-shaye, kai har ma fyade ana yi a ciki.
“Mun kai korafi ga ma’aikatar muhalli ta jiha tun sama da shekara goma, inda suka yi alkawarin za su zo amma har yau ba labari.
‘Ko da yake daga bisani an fara aikin daga unguwar Tukuntawa amma da aka zo Sabuwar Gandu sai aikin ya tsaya ba tare da ya karaso yankinmu ba”, inji shi.
To sai dai da muka tuntubi Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano ta ce tana sane da matsalar zaizayar kasar kuma tana kokari ta hanyoyi da dama wajen ganin ta magance ta.
Babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Garba Saleh Ahmad ya ce, “Tuni muka fara wani gagarumin aikin gina matatun da za su kawo karshen matsalar dagwalon masana’antu.
“Wani aiki ne na makuden kudade da zai samar da matatu guda uku a unguwannin masana’antu na Sharada, Challawa da kuma Bompai.
“Aikin ya samu taimako ne daga Gwamnatin Tarayya ta hanyar tallafin da ta ke bayarwa don bunkasa kalubalen muhalli.
“Za mu giggina manyan kwatoci kuma rufaffu da za su rika dauko wannan dagwalon daga masana’antu zuwa wadannan matatun ta cikin manyan fayif da muka riga muka sayo.
“Da yardar Allah da zarar mun kammala wannan matsalar za ta zama tarihi”, inji babban sakataren.
Dakta Garba ya yi kira ga al’ummar yankunan da su kara hakuri yayin da aikin ke ci gaba, yana mai cewa tuni rukunin farko na aikin ya riga ya kammala.
Sai dai ya yi kira gare su da su guji zubar da shara a cikin hanyar, domin hakan na kara taimakawa wajen ta’azzarar matsalolin yankunan.