A ranar Juma’a za a gudanar da zaben shugaban kasa a Libya, sai dai mutane kadan ne ke ganin zaben zai gudana sakamakon yakin basasa da rarrabuwar kawuna da kasar ke fama da su.
Ana ganin cewa wannan zabe da za a ayi wata nasara ce da aka samu tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Muammar Gaddafi da aka yi a shekarar 2011 bisa amincewar Majalisar Dinkin Duniya.
- Koriya ta Arewa: Yadda ake bikicin cika shekara 10 da mulkin Kim Jong Un
- Cutar Zazzabin Lassa ta kashe mutum 80 a Najeriya —NCDC
Sai dai akwai alamun tambaya sosai dangane da yiwuwar zaben, duba da yanayin rashin tsaro da kasar ke fama da shi ba ba zai ba da damar gudanar da zaben yadda ya kamata ba. Ko me zai faru?
— Shin zaben zai gudana?
Duk da cewa an sanya zaben a ranar Juma’a, amma har yanzu akwai ’yar takaddama dangane da yadda zai wakana.
A watan Satumba dai Shugaban Majalisar Dokokin Libya, Aguilah Saleh, ya zartar da wata doka, wadda ta bai wa abokinsa Khalifa Haftar damar tsayawa takara.
Duk da cewa a Yammacin kasar ba son Haftar din sakamakon shafe shekara guda ana kai hari kan babban birnin kasar Tripoli a shekarar 2019-20 amma bai damu da kai wani dauki yankin ba, sai dai kawai ya maida hankali a Gabashi da Kudancin kasar.
Bugu da kari an sanya dokar hana bayyana ’yan takara har sai saura mako biyu da zabe; Amma ko a ranar Asabar din a makare a aka bayyana sunayen ’yan takarar, lamarin da ya sa ake ganin ba za a gudanar da zaben a kan lokaci ba.
— Ya kuma batun tsaro a kasar?
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da dama sun bayyana cewa a halin da ake ciki babu alamar gudanar da sahihin zabe a kasar.
Kuma duk da tsagaita bude wuta da aka kwashe tsawon shekara guda ana yi, lamarin tsaro da yawan zirga-zirgar dakarun tsaro zai iya haifar da fargabar sake komawa cikin rikici.
A cikin ’yan makonnin da suka gabata, wasu mutane dauke da makamai sun hana shiga wata kotu a Sebha inda ake shari’ar daukaka karar da hukumar zaben kasar ta yi, wadda ta yi watsi da bukatar Seif al-Islam Gaddafi dan tsohon Shugaba Gaddafi da aka kashe.
Duk da cewa a karshe sun janye kuma kotu ta dawo da takararsa, amma lamarin ya sa gwamantin nuna damuwarta a kan hakan.
Wannan ya sa Ministan Harkokin Cikin Gida, Khaled Mazen, ya yi gargadin cewa gwamnatin wucin gadi ba za ta iya tabbatar da tsaro yayin zaben ba.
Har ila yau, ana zargin Haftar da yunkurin haifar da mulkin kama-karya na soji, kuma ana gani mazauna gabashin Libya ba za su iya kada kuri’ar adawa da shi cikin aminci ba.
Tsohuwar mamba a Kwamitin Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Libya, Amanda Kadlec ta ce, “Mafi karancin abubuwan da ake bukata domin gudanar da zabe na gaskiya da adalci babu su a halin yanzu.”
Haka kuma, ana zargin har wasu sun samu takardun kada kuri’a tun gabanin zaben wanda yake nuna tuni wasu sun shirya wa magudi a zaben.
Har wa yau, wasu mutanen da ke da muradin kada kuri’a sun koka a shafukan sada zumunta cewa sun je karbar katin zabe, amma sai suka ga har an riga an karbe su.
— Shin za a yarda da sakamakon zaben?
Ko da an gudanar da zaben lafiya ba tare da wata matsala ba, ba lallai ba ne kowane bangare ya yarda da sakamakon.
Abokan hamayyar, kowanne daga cikin ukun da ake ganin na kan gaba sun sanya shakku kan takararsu kuma kowannensu yana da dakarun da ke goya masa baya.
Bugu da kari, mutane kadan ne daga Yammacin kasar za su amince da nasarar Haftar.
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na neman a kama Seif al-Islam Gaddafi da laifin cin zarafin bil-Adama, kuma an yi karar shi a kotunan Libya saboda irin wadannan dalilai.
Shi ma Abdulhamid Dbeibah, kafin a nada shi Fira Minista na rikon kwarya, ya sha alwashin ba zai tsaya takara ba kafin daga bisani ya yi watsi da alkawarin.
— Kalubalen da ke gaban gwamnati mai zuwa?
Ba ma wannan gwamnatin da za ta karbi mulki bayan gwamnatin da ta yi mulki sama da shekara 40 ba, duk wata gwamnatin farar hula da ya kasance ta karbi mulkinta daga hannun gwamnatin mulkin mallaka dole ne ta fuskanci kalubale mai yawa saboda yanayin yadda aka gudanar da mulkin a baya.
Babban abun tambaya shi ne, shin gwamnati mai zuwa za ta iya hada kan cibiyoyin gwamnati ciki har da babban bankin kasar da ya rabu a shekara ta 2014 yayin da gwamnatin da ke gaba da juna ta karbi mulki a Gabashin Libya.
Shin hade ko wargaza dakarun kasar da ke yaki da juna har zuwa tsakiyar shekarar 2020 za’a yi ko ya ya, wanda hakan babban kalubale ne musamman yadda wasu mayaka ‘yan kasashen waje kusan 20,000 ke ci gaba da zama a kasar Libiya.
Samar da kundin tsarin mulki shi ma wani babban kalubale ne wanda rabon kasar da amfani da wani kundin tsarin mulki tun bayan da tsohon shugaban kasar Gaddafi ya yi watsi da kundin a shekarar 1969, kuma rashin wannnan kundi shi ya kawo duk ire-iren kalubalen da ake samu a dokokin zaben da ake shirin gudanarwa.
Ga talakawan Libya kuma, abubuwan da suka fi bukata su ne: a yi maganin matsalar tsaro, a farfado da tattalin arzikin kasar, a kuma sake gina kayayyakin more rayuwa da yaki ya lalata da kuma kawo karshen katsewar wutar lantarki.
Har ila yau, matsalar Libya da manyan kasashen Turai kan batun bakin hauren Kudancin Afirka da ke amfani da kasar a matsayin tudun-mun-tsira na neman shiga Turai, wanda shi ma ba karamin babban kalubale ba ne.
Kungiyoyin kare hakkin bil’Adama da dama na ganin dole kungiyar Tarayyar Turai ta tashi tsaye wajen tunkarar matsalar safarar mutane da mugun cin zarafin da mutanen ke fuskanta a hannun masu safarar.