✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda zaben kananan hukumomin Kaduna ke gudana

Na'urar zabe ta bayar da matsala a wasu rumfunan zabe.

A yayin da da kayayyakin zabe ke suka isa mazabu a Karamar Hukumar Jama’a, a karamar hukumar Kaura tuni aka fara aikin tantance masu kada kuri’a.

A mazabar 008 da ke kauyen Mahuta mai suna Manchok/Buba Duniya a karamar hukumar Kaura, wakilin Aminiya ya ga yadda na’urar ta ki karbar katin zabe guda uku da aka gwada.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi jami’ar da ke kula da aikin zabe a wurin, Leah Nache, ta ce bata san dalilin da ya haifar da haka ba, amma za ta kirawo lambar da aka ba su don aikawa da koken da suka ci karo da shi.

A mazabar Ninyo Ala, mazabar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex, kuwa da ke Randiyem a Manchok, shi ma da ke Karamar Hukumar Kaura, jami’in da ke kula da zaben, Mark Jerry, ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya tsaf don fara aikin tantancewa, amma saboda matsalar da suka ci karo da shi a na’urar fitar da takardar da ke dauke da komai da ya shafi bayanan na’urar ta sa sun dakata.

“Mun kira lambar wayar da aka ba mu don sanar da duk wata damuwa da ta shafi na’urar ba ta shiga, amma na tura da sakon kar-ta-kwana.” inji shi.