Da yawan mata sun rasa gano bakin zaren yadda za su sahihiyar hanyar da za ta sa namiji ya so su so na gaskiya.
Wasunsu sun dauka kyau da kwalliya ne kadai maganadisun mace na yi wa soyayyar da namiji kamun kazar kuku.
Eh toh! Suna cikin abubuwan da kan karkato da wasu mazan, amma kuma maza sun bambanta ta fuskar ababen da suke so a tattare da mace, duk da cewa akwai wasu abubuwan da suka yi tarayya a kai.
Wasu maza da muka zanta da su sun fede mana biri har wutisya game da abubuwan da kan sa su nutse a kaunar mace. Ga biyar daga ciki:
– Kunya
Ki kasance kin dabi’ar jin kunya domin siffantuwar ki da kunya babban ado da ke saurin jan hankalin namiji ya ji kaunar ki ta mamaye zuciyarsa.
Kar ki sake ki zama daga cikin fitsararrun mata domin babu namijin kirki da zai so ki kasance uwar ’ya’yansa. Na tabbata ke kanki mutumin kirki za ki so ki aura.
Wani matashi da muka zanta da shi, Abdulrahim Ushata ya ce, “Za ki yi ta jin ana cewa ai maza ba su son mace mai kunya, kunya na cutarwa.
“Wannan duk zancen mutane ne, kunya ita ce ke kara daraja da martabar ’ya mace.
“Kunyarki ce za ta sa mutum ya ji kullum yana kara son sanin wani sabon abu game da ke saboda kunyar za ta sa ya ji yana fahimtar abin da kike so kuma zai yi ta kokarin jan ki a jika da kuma tarairayar ki.
“Hakan zai sa kullum soyayyarku ta yi ta kara armashi, kamar a ranar kuka hadu saboda kullum sabon abu ne zai gani a tattare da ke.”
– Ilimi da hazaka
Abubakar Salis ya bayyana wa Aminiya cewa maza na son mace mai ilimi da himma da kuma fahimtar al’amuran yau da kullum.
Ki kasance kin fahimci al’amuran da suka shafi rayuwa, musamman a cikin al’umma ta yadda za ki yanke hukunci yadda ya dace; Kar ki yadda ki zama kifin rijiya, wadda dan kankanin abu ma sai ya daure mata kai.
“Ba lallai sai kin rika fitowa da sakamakon jarabawa mafi kyau ba, ya dai zama ke ba sakarya ba ce, kina da ra’ayinki kuma a duk inda kike za ki iya bayyanawa ba tare da fargaba ba, sannan ya zama kina da sani a kan abubuwan da ke wakana a rayuwa.
“Ki san abubuwan da suka shafi kasarki da za ku iya zama ku tattauna a kai; Hakan ba zai sa ku gundurar juna ba saboda ko ba zancen soyayya ba, akwai abubuwan da ku ke tattaunawa a kai.”
– Fara’a
A cewar Imran Gambo, mace mai fara’a ta fi saurin burge namiji sama da wadda za ta fito fuskarta a daure babu fara’ ko miskala-zarratin.
Imran ya ce mata marasa fara’a na saurin gundurar mutum kuma ba sa raina abin yin fada a kai sannan ga saurin fushi.
Sai dai ya ce, “Idan an ce mace ta zama mai fara’a ana nufin ta kasance mai sakin fuska ne amma ba ta zama sakarya tana bude hakora barkatai ba; ya dai zama fuskarki a sake take yadda ba za ta firgita mutane ba.
“A Musulunce ma ai murmushi sadaka ne, saboda murmushin da aka raina kan iya zama sanadiyar yayewar damuwar wani,” inji Imran.
– Tausayi
A cewar Muhammad Umar, tausayi dabi’ar mutanen kwarai ce shi ya sa ake so mace ta kasance tana da shi.
Ya ce idan namiji ya fahimci cewa akwai tausayi a zuciyar mace, hakan na kara narkar da shi a cikin kaunar ta.
“Tausayin kuma ya zama ba a kansa kadai ba, har a kan sauran mutane, musamman in ya ga kina son taimakon mutane.
“Hakan zai kara masa son ki saboda ya san cewa ba shi kadai ba, ’ya’yansa ma sun yi dacen uwa ta gari mai tausayi.”
– Son yara
A cewar Rufai Ahmad, “a matsayinki na mace yana da kyau a ce kina da kyakkyawar mu’amala tsakaninki da yara saboda wata rana za ki zama uwa ke ma.
“Ina son mace mai son yara. In na ga tana wasa da su yakan kayatar da ni, saboda a lokacin ne wasu abubuwa game da ita ke bayyana, musamman yadda za ta mayar da kanta daidai da yanayin da yaran za su ji dadin kasancewa tare da ita.
“Hakan shi zai nuna ma shi cewa yaran shi sun yi dacen uwa.”
Kadan ke nan daga cikin abubuwan da maza ke so a tattare da mace.
Ina fatan wadanda suka karanta za su amfana da abubuwan da aka lissafo, za su kuma yi aiki da su.