A lokacin da matashiya Hauwa ’yar unguwar Fagge take tsaka da shirin fara aiki a Babban Bankin Nijeriya (CBN), ne ta koma neman aikin dan sanda. A kwana a tashi, yanzu ta kafa tarihi, inda ta shigar da Jihar Kano cikin jerin ’yan tsirarun jihohin da mata ’yan asalin jiharsu suka kai mukamin kwamishinan ’yan sanda a Nijeriya.
A tattaunawarta da Aminiya, wannan bakanuwar kuma kallabi tsakanin rawuna, CP Hauwa Ibrahim ta bayyana yadda rayuwa ta kasance mata tun daga kwalejin horon ’yan sanda da irin gwagwarmayar da ta sha, da abin da ya ba ta kwarin gwiwa, da kuma burinta na nan gaba…
Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Za ki iya ba mu labarin rayuwarki da abin da ya ba ki kwarin gwiwar shiga aikin dan sanda?
Suna na Huawa Ibrahim, ni ’yar Kano ce, daga Karamar Hukumar Fagge. Na tashi a layin ’Yan Katifa Kwarin Gogau, na yi makarantar Firamare a Fagge, na gama na shiga GGC Dala na gama, na ci gaba da makarantar gaba da ta CASS a Zariya. Daga nan na yi karatun share fagen shiga jami’a da ake kira IJMB, bayan na yi nasara sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya aka ba ni kwas na karantar Kimiyyar Siyasa inda na kammala A 1995, sai na yi bautar kasa a garin Kano inda na yi aikin a Babban Bankin Nijeriya (CBN) shi ma na kammala a 1996, sai Allah Ya kawo harkar shiga dan sanda.
Kamar yadda na shaida maka. ni ina tunanin cewa CBN za su bani aiki, wata rana ina zaune sai na ga sanarwa cewa hukumar ’yan sanda na neman masu sha’awar shiga aikin da suka gama sanannun jami’o’i na Nijeriya da su je a tantance su, to daga nan ne sai na yanke shawara na ce bari in gwada kafin CBN su ba ni aikin da nake sa rai zan samu, sai na tafi da niyyar ko da wata uku ne in yi kafin wannan aikin na CBN ya fito. Daga shiga ta ofishin ’yan sanda sai aka tarbe ni da murna ana ganin ga bakanuwa za ta shiga aikin dan sanda, abin ya ba ni mamaki kamar suna jiran in zo ne.
Aka kai ni wajen kwamishina na wannan lokaci ana kiran sa CP Hashim, Allah ya gafarta masa, ya tambaye ni cewa lallai zan iya wannan aiki? Na amsa masa da cewa zan iya, na amsa ne saboda na riga na shigo amma ban san me zan je in tarar ba, ina nufin yanayin horon da zan samu, don ni dai a lokacin dan sandan da na sani shi ne kurtu da sajen da muke gani koyaushe a bakin hanya, ban san da wasu manyan ofisoshi na wannan aikin ba a wannan lokacin.
Cikin ikon Allah sai da CP ya bayyana min cewa idan na shiga zan fito da anini daya, har ya sa aka kira mai anini daya, aka gwada min shi, daga nan fa aka ce ai na samu wannan aiki, ganin cewa na zo daga Arewa kuma ga ni mace. Daga nan fa sai aka fara shirin shiga aiki, muka yi tantancewa har sau uku wadanda duka na samu sa’ar tsallakewa daga karshe dai mu ’yan Kano mutum 10 ya samu wannan aiki a wannan shekarar, amma ni kadai ce mace.
Haka na shiga fa aka fara ba mu horo, abin da ba mu taba tsammani ba, don abin da muka gani a wajen horon nan ya yi kama da abin da ake yi a fagen yaki, amma mun sha horo mai wahala da tsanani don tun karfe 4 na safe za mu tashi mu kama ayyuka kala-kala daga gudu zuwa tsalle-tsalle da dai suran ayyuka na horon aikin dan sanda.
A matsayinki na mace, wane kalubale kika fuskanta a wannan aiki?
Kalubale na farko da na fuskanta shi ne abin da ya shafi sutura, ashe a nan buje ne ake sakawa ni kuma ’yar Kano Bahausa Musulma abin sai ya zama bako, ga kuma tsari da tarbiyya irin ta Musulunci kuma a Arewa, sai na fara tunanin cewa idan fa na gama karbar horo dole ne in rika sanya shi, sannan sauran mutane ganin cewa ba su saba ganin mace a cikin wannan aikin ba, sai wasu ke mana kallon marasa tarbiyya ko mutanen banza, don wasu har ce mana suke yi wai wannan aikin na karuwai ne. Muka yi korafi dangane da sanya buje wanda daga karshe aka sahale mana mu rika sanya dogon wando. Kamar yadda na fada maka, mu hudu ne mata daga Arewa, akwai wata daga Adamawa sai wata daga Maiduguri sai wata daga Katsina, sannan ni daga Kano. Da kwarin gwiwar da manyana suka ba mu muka samu cikakken horo na aiki kuma muka gama.
Yaya rayuwa ta kasance a kwalejin horon aikin dan sanda gareki?
Da farko dai an kai mu kwalejin horar da ’yan sanda ta Kano ga shi mun yi jami’a mun gama a yanayi na ’yanci da saukin rayuwa, sai ga mu a wani sabon wuri ba ’yancin fita lokacin da kake so, sai horo iri-iri sannan rayuwa a wannan wuri sai da aka koya mana komai har tafiya da magana an koya mana yadda za mu yi, rayuwa ta zama sabuwa gaba daya.
Ta yaya kalubalen da kika fuskanta ya shirya ki zuwa wannan matsayi da kike a kai?
Wannan ya sanya na samu fahimtar bambance-banbancen da muke da su a Nijeriya sannan na zama mai fahimtar cewa duk abin da ka saka a gaba idan dai ka yi kokari ka yi shi da kyau to zai taimake ka ka cim ma burinka a duniya.
Ke ce mace ta farko da ta kai matsayin kwamsihinan ’yan sanda daga yankin Arewa maso Yamma, ya kika ji da aka shaida miki cewa kin samu wannan matsayi?
Gaskiya na ji dadi sosai, in na tuna lokacin da muke karbar horo a kwaleji muna ganin wahala ta yi yawa tun da dukanmu ba mu saba ba ganin inda muka fito, ban taba tsammanin cewa Allah Zai kawo ni wannan matsayin ba, don wannan shi ne kololuwa na aikin dan sanda, duk wanda ya taka wannan matsayi to sai dai sanbarka. Burin duk wani mai aikin dan sanda a ce yau ya zama kwamishinan ’yan sanda. Cikin ikon Allah bayan fuskantar kalubale iri-iri da wahalhalu sai ga shi an wayi gari an kira ni don a kara man wannan matsayi, ai gaskiya murnar ma ba ta kwatantuwa, abu ne wanda ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwa.
Wanne sako za ki ba wa matasa mata ’yan Arewa da suke fatan cimma nasarori a aikin tsaro da sana’o’in da aka saba ganin maza sun mamaye?
Shi dai wannan aiki gaskiya na maza ne tsakani da Allah, saboda akwai kalubale wanda za ka ga mazan ma su ne ke fuskantar shi, amma mu muna taimakawa ne. Sannan duk wani abu mai wahala kamar yadda muka yi karatu na jami’a ka san idan ba ka dage ba ka san ba za ka ci ba, to shi ma abu ne wanda yake bukatar jajircewa. Idan ka yi niyyar wannan aiki, to ka sani cewa ka shirya wa duk wani abu da zai bijir ona wahala ko akasin haka, sannan ka sa a ranka cewa wata rana ku ne manyann gobe, to hakan zai ba ka damar ka cimma duk burinka na zama abin koyi ko abin buga misali kamar yadda a yanzu mutane da dama wadanda ma ban san su ba suna ta min fatan alheri suna taya ni murna.
Yaya kike ganin nadinki zai canza tunanin jama’a game da mata a fannin aikin ’yan sanda a Nijeriya?
Ina fatan wannan matsayi da na kai zai canza tunaniun mutane da yawa musammam daga Arewaci na ganin cewa aikin dan sanda ba na maza ba ne kawai. Kamar yadda ka sani Hausawa sun ce, “Nagari na kowa,” kafin ka zama nagari za ka taka matakai sannan daga karshe ka zama abin koyi da kwatance a wurin mutane. Lokacin da muka shiga babu mutanenmu, ni ma Allah Ya kaddara ne kawai, don ni ban taba samun wata mai irin wannan aikin ba da na ji ina son in zama kamarta ba a tsawon lokacin da na yi kafin in fara wannan aikin, babu wadda ta ba ni kwarin gwiwar shiga dan sanda, don yawancin mata a wannan aikin ’yan Kudu sun fi yawa, to ka ga bambanci irin na al’ada da addini ba zai bari mu kwaikwaye su ba, tunanin cewa wata rana cikin ikon Allah za ka zama wani abu idan ka yi hakuri, muddin ka saka hakuri da jajircewa to komai a duniya lokaci ne kawai yake jira.
Mene ne burinkin a matsayinki na Kwamishinar ’Yan Sanda a inda da aka ba ki aiki?
Daman aikinmu aiki ne na tsaro duk maganar ta tsaro ce, ya za a inganta shi a kowane mataki? Da wa za ku hada hannu ku samar da wannan kuma shi ne tare da mutanen gari. Abin da nake so shi ne duk inda Allah Ya kai ni in samu yadda zan inganta tsaron wurin tare da hadin kan al’ummar wannan wuri.
Wane irin manyan kalubale kika fuskanta a aikinki a matsayin mace, kuma ta yaya kika shawo kansu?
Na fuskanci kalubale iri-iri kuma kamar yadda nace ana shawo kan kalubale ne ta hanyar jajircewa da kyakkyawar niyya da tsayawa kan gaskiya. Yawanci maza suna da kishi idan an hada su aiki da mata to wannan ya zama cikin kalubalen da ya kara min kwarin gwiwa. Wani lokaci sai maza su rika ganin kamar don kina mace ba ki iya wani aikin wanda kuma ba haka ba ne, kuma akwai danniya daga bangaren maza a kowane mataki, amma jajircewa da aiki tukuru duk yana sanya mutum ya ci nasara.
Za ki iya ba mu labarin wani babban abin da kika cimma a aikinki wanda ya yi miki tasiri mai girma a matsayinki na ma’akaciyar tsaro?
Wannan babbar nasara ba ta wuce samun matsayin da nake kai a yanzu ba, wanda ni dai ban taba tunanin zan kai ba. Ban ma shiga aikin da tunanin zan zauna in yi shi ba, don ni a lokacin ina tunanin aikin CBN ne, da yake Allah Ya tsara wannan, ga shi yau ni ce aka yi wa mukamin CP.
Kin taba fuskantar nuna wariya ko kyama saboda jinsinki?
Akwai wariya da kyama da na fuskanta daga abokan aiki ganin cewa ni mace ce, amma hakuri da dogewa da daukar shawarwari irin na manyanmu na wajen aiki sun taimaka duk wannan bai yi wani tasirin a zo a gani ba.
Wane kira ke gare ki ga al’ummar Nijeriya gaba daya?
Kirana ga al’ummar Nijeriya shi ne mu rike kasarmu ta gado, ba mu da wata kasa da ta fi ta, don a iya sanina babu wata kasa a duk duniya kamar Nijeriya. Lallai muna da matsalolinmu, amma idan muka sanya kishin kasa da gaskiya to za mu ceto ta daga fadawa cikin mawuyacin hali. In har za mu yi kishin kasa da gaske to kasarmu za ta zama daya daga cikin manyan kasashen duniya. Matsalarmu kawai wasu halaye irin mamu da ba su da kyau, mun san su to ya kamata mu gyara don kasar mu ta gyaru.