Gwamnatin Zamfara ta bayyana matakan da mutanen da ke bukata za su bi domin samun lasisin mallakar bindiga a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ce an tsara abin ta yadda za a tabbatar da karin bindigogi ba su fada hannun bata-gari ba.
- Satar kifi ta jawo wa matashi daurin wata daya a kurkuku
- ’Yan Najeriya za su fara biyan harajin N10 kan lemon kwalba
Matakan a cewarsa su ne:
- Mutum zai fara cika fom din neman lasisin mallakar bindiga
- Za a cika fon din ne a matakin unguwanni
- Masu sarautun gargajiya za su tantance masu neman lasisin
- Ba za a ba wa bata-gari ko wadanda suka taba aikata babban laifi ba
- Daga nan za a tura takardun ga Kwamishinan ’Yan Sandan jihar
- ’Yan sanda za su gudanar da binciken su tantance su
- Sai a tura wa Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya kara tantancewa
- Daga nan sai ya ba wa mutanen da suka dace lasisin mallakar bindiga
Dosara ya bayyana cewa duk da cewa gwamnatin jihar ta umarci mutanen su tashi su mallaki bindigogi domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga a jihar, haka ba ya nufin duk wanda ya nema zai samu kai-tsaye.
Ya yi karin hasken ne bayan kurar da ta biyo bayan umarnin gwamnatin jihar, inda wadansu ke ganin ba da lasisin mallakar bindiga barkatai zai yi mummunar illa.
A karshen mako ne gwamnatin jihar ta sanar umarci Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da ya fara shirye-shiryen bayar da lasisin mallakar bindiga ga duk wanda ke bukata a jihar.
Sanarwar da Dosara ya fitar ta kara da cewa za a ba wa kowacce daga cikin masarautu 19 da ke jihar fom guda 500 domin masu bukatar iznin mallakkar bindiga.