✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a yi kwalliyar mai ma’ana

Mata da dama ba su san yadda za su kintsa kansu ba. Da zarar sun yi aure sun haihu daya sai su karaya da irin…

Mata da dama ba su san yadda za su kintsa kansu ba. Da zarar sun yi aure sun haihu daya sai su karaya da irin kwalliyar da suke yi wa maigida. To kada a manta cewa maigida fa yana zuwa aiki kuma a hanyarsa ta aiki akwai mata kyawawa da dama. Ko da ke kyakyawa ce sai ana hadawa da wanka da kuma kwalliya mai ma’ana. Don haka, a yau na kawo muku yadda ake yin kwalliya mai ma’ana.
•A tabbata an wanke fuska da sabulun wanke fuska kamin a fara kwalliya a fuska. A busar da fuskar kuma da tawul mai kyau kamin a shafa wa fuskar komai.
• Kada a rika wanke fuska da ruwan zafi sai dai ruwan dumi domin yin haka yana sanya fuskar ta zama mai gautsi.
• Daga nan za a iya amfani da irin daya daga cikin su hadin da nake kawo muku a fuska domin magance kurajen fuska
•Sai a shafa man fuska musamman mai dauke da sinadarin SPF na kare kunan rana domin kare fuskar daga zama mai lalura. A tabbata cewa man ya shiga fatan sosai ya kuma bushe a fatar kafin a yi wa fuskar komai.
•A shafa hodar fandesho a fuska kuma a tabbata ta shafu a duk fuskar baki daya in ba haka ba, zaa ga fuskar ta zama kala daban-daban.
•Sannan sai a shafa hoda daidai kalar fatar. Domin a kara hasken fuska.
• Bayan hakan, sai a shafa gazal a ido wadda ta dace da ido
• A kuma sami jan baki musamman mai jan kala domin wannan kalar na dacewa da mace mai kowace irin kalar fuska.