✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a yi gasar Premier ba tare da ’yan kallo ba

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ingila, Greg Clarke, ya ce ba ya tunanin za a kyale magoya bayan kungiyoyi su shiga cikin filayen wasa ‘nan da…

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ingila, Greg Clarke, ya ce ba ya tunanin za a kyale magoya bayan kungiyoyi su shiga cikin filayen wasa ‘nan da dan kankanin lokaci’, sannan ya yi gargadin cewa annobar coronavirus za ta jawo wa hukumar asarar kimanin fam miliyan 300.

An dakatar da wasannin kwallon kafa a duk fadin Ingila har sai abin da hali ya yi, yayin da aka sanar da karkare dukkanin kananan rukunonin gasar kwallon kafar da suke kasa da mataki na hudu, wato division four.

Ana kuma fargaba game da kakar wasan shekarar 2020/21 sakamakon ka’idar nan ta nisantar juna da za ta yi wa gasar illar gaske.

Za a tafka asara

“Alal misali, yana da matukar wahala a iya ganin cikowar ’yan kallo magoya bayan kulob-kulob – wadanda su ne karsashin wasannin – cikin kankanin lokaci a filayen wasa,’’ a cewar shugaban.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ana sa ran karasa ragowar wasannin Premier League din ba tare da ’yan kallo ba, yayin da aka yi kiyasin tafka asara ta kimanin fam biliyan guda – idan har ba a karkare kakar ta bana ba.

A ranar Juma’a ne aka sanar wa manyan kulob-kulob din gasar Premier cewa za a karasa sauran wasannin a filayen wasannin da ba na kowane kulob ba.

Anya wasannin kwallon kafa za su yi armashi kuwa idan babu ’yan kallo?

Hakan koma-baya ne

A cewar Aminu Halilu Tudunwada, marubucin labaran wasanni ne da sharhinsu a Kano, hakan ba karamin koma-baya ba ne saboda wasu dalilai.

“Ba karamin koma-baya bane ga su ‘yan kallo wadanda suke sayen tikitin wasanni na shekara guda.

“Sannan a gefe daya kuma su ne ke samar da kashi 70 cikin 100 na kudin shiga ga kungiyoyin da suke goyon baya, hakan ya sa dole mahukunta a kasar ta Ingila su yi dari-darin yadda gasar za ta gudana ba tare da ‘yan kallo ba”, inji Aminu Tudunwada.

Ya kuma kara da cewa “su kansu ‘yan kallo da magoya baya wannan yanayin zai zo musu banbarakwai, kasancewar hakan bai saba afkuwa ba a ce ana wasanni ba ’yan kallo kuma ba za su mara wa kungiyoyin da suke so baya ba, wanda hakan zai rage karsashin gasar tare da sare gwiwar da yawan ‘yan wasan da suke wakiltar kungiyoyin daban-daban, duba da amfani da kuma kimar ’yan kallon da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen kambama kungiyoyinsu da kuma goya musu baya, a cikin yanayin da suke walau na nasara ko akasin hakan”.