A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar watan Azumi na shekarar 1443 bayan Hijira, hukumomin da ke kula da masallacin Annabi Muhammad SAW a birnin Madina, sun fitar da tsare-tsaren buda baki na bana.
Tsare-tsaren sun hadar da ka’idodin yadda masu bayar da sadakar abinci da masu buda baki kamar yadda hukumar gudanarwar masallacin ta bayyana.
- Iran da Saudiyya na daf da maido da huldar diflomasiyya
- Saudiyya ta musanta shirin dakatar da Umara a yanzu
Ga dai ka’idodin da mahukuntan suka fitar kamar haka:
- Za a bar wadanda suke da lasisin kawo abincin shan ruwa su ci gaba kamar yadda suka saba a baya.
- Za a kididdige yawan jama’ar da ake bukata wajen buda bakin.
- Masu rabon abinci za su tuntubi kamfanonin da aka yarjewa dafa abinci domin su shirya masu abincin da za su bayar.
- Mutum biyar ne kawai za su zauna a kan kowace shimfida idan akwai bukatar ba da tazara yayin gudanar da buda bakin.
- Mutum 12 kacal aka bai wa damar zama idan ba a bukatar bayar da tazara yayin buda bakin.
- Dole a zauna bangaren da za a fuskanci alkibla kadai.
- Sabunta bayanai zai fara ne daga watan Rajab.