Kwalejin Harshen Larabci na Sarki Salman da hadin gwiwar Ofishin Jakadancin kasar Saudiyya da ke Birnin New York a Amurka ya shirya taro a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya domin bikin Ranar Harshen Larabci.
Karo na Hudu a jere ke nan da ake gudanar da taron da nufin raya harshen Larabci a manyan hukumomin duniya da kuma tallata matakan da Saudiyya ke dauka domin raya harshen wajen bunkasa al’adu da kuma kimiyya.
Taken bikin na bana, wanda zai gudanar a ranar Litinin 9 ga Dismaba, 2024, shi ne ‘Harshen Larabci da Fasahar Na’ura – Bunkasa Kirkire-Kirkire tare da Raya Al’adu.
Kamfanin Dillancin Labaran Kasar Saudiya (SPA) ya bayyana cewa Ministan Raya Al’adun kasar, Yarima Badr bin Abdullah bin Farhan ne mai masukin baki a wurin taron, wanda zai karbi bakuncin manyan shugabanni da jami’an diflomasiyya.
- Lawan ya bai wa waɗanda gobara ta shafa tallafin 10m a Yobe
- Shugabanci: ’Yan Arewa su jira sai 2031 —Akume
- An kashe yawancin hakimaina a rikicin Boko Haram —Shehun Borno
A taron na bana za gudanar da tattaunawa kan ‘Fassarar Larabci a Majalisar Dinkin Duniya’ inda kwararru daga sassan duniya za su tattauna tare da bayar da kwas kan ‘dabarun fassarar harshen Larabci a harkoikin diflomasiyya, ga ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya.
Kazalika an shirya baje kolin kayan zayyana da al’adu da tarhin Larabawa da cigabansu, musamman daga yankin Saudiyya.