Sau da yawa za a ga baki na wari musamman da safe ga wadanda ba su ci abinci ba. Wani duk da ya wanke bakinsa da magogi da man goge baki, hakan ba ya korar masa da warin bakin.
Kuma ba zai san cewa bakin nasa na wari ba. To idan ana son a san cewa baki na da wari ga irin abin da za a yi don tabbatar da bakin na da wari:
- Yadda za a yi bankwana da warin baki
- Takaddamar soyayya:Tsakanin maza da mata wa ya fi rikon amanar soyayya?
• A lashe bayan hannu sai a jira na tsawon minti 10 sannan sai a sunsuna a baki sannan a fitar da iska sai a tare iskar da hannu sannan sai a sunsuna in da wari to ana da warin baki.
• A tambayi kawa/aboki, maigida da kuma ’ya’ya don sanin ko ana da warin baki.
Ababen da ke rage warin baki Cin cingam mara sukari:
Cin cingam na rage warin baki musamman cingam wanda ba shi da sukari. A tabbatar da cewa cingam din ba ya da sukari, kasancewar cingam mai sukari na sa baki wari, domin kwayoyin bakteriya da ke bakinmu na son sukari kuma yin hakan zai sa bakin wari sosai.
Shan ruwa sosai:
Busasshen baki na da wari. Shi ya sa baki ya fi wari da safe don bakin ya jima a rufe ba tare da an ci wani abu ba. Shan ruwa na rage warin baki. Kada ki bar bakinki a bushe.
Cin ayaba
Idan ana kokarin rage kiba ne, za a iya cin ayaba, inda hali yawan cin ’ya’yan itace. Yin hakan na rage warin baki.
Wanke baki a kan lokaci:
A zama mai wanke baki da safe da yamma don rage warin baki. Akwai lunguna da yawa wadanda abinci ke makalewa a tsakanin hakora.
Babban abin da ke janyo warin baki shi ne barin ragowar abinci a lungunan hakora. Wanke baki na da muhimmanci sosai in kuwa ba an yi haka ba za a gujewa warin bakinsa.