✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu rage mace-macen mata wajen haihuwa — Gwamnan Kano

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar inganta harkar kiwon lafiya a kowane mataki a jihar.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da ƙananan yara na shekarar 2024 a hukumance.

Gwamnan, ya ƙaddamar da makon ne a Asibitin Kula da Mata da ƙananan yara da ke Tarauni.

A jawabinsa, gwamnan ya jaddada cewa makon lafiyar mata da ƙananan yara na da burin inganta kiwon lafiyarsu, ta hanyar mayar da hankali da ɗaukar matakan rigakafi da magance cutar da ke addabar iyaye mata da yara.

Ya ƙara da cewa, taron na tsawon mako guda wata dama ce ga mata da ƙananan yara, domin su ƙara samun kulawa ta hanyar tsarin kiwon lafiya da ake da su, wanda ke ƙara ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta da ake samu a ƙanana da manyan asibitocin jihohin jihar.

Gwamnan, ya ce Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar al’ummarta.

Kazalika, ya nanata ƙudirin gwamnatinsa na rage mace-macen mata da ƙananan yara da kuma magance cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro da cuta mai karya garkuwar jiki da tarin fuka.

Tun da farko Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa manufar makon kula da lafiyar mata da ƙananan yara, shi ne samar da cikakkiyar kulawa ga mata masu juna biyu tun daga ɗaukar ciki har zuwa haihuwa da kuma tabbatar da jin daɗin jarirai da yara ‘yan kasa da shekara biyar.

Dakta Labaran, ya bayyana jin daɗinsa da yadda gwamnan jihar ya jajirce wajen kula da fannin kiwon lafiya tare da bayar da tabbacin cewa ma’aikatan lafiya a Jihar Kano sun ƙuduri aniyar samar da ayyuka masu inganci ga al’umma.

Taron ya samu halartar wakilin Sarkin Kano, Turakin Kano kuma Hakimin Dala, Alhaji Abdullahi Lamido Sanusi, da wakilan ƙungiyoyin bayar da tallafi a ɓangaren lafiya da suka haɗa da Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Ƙasa da Asusun Tallafawa Kananan Yara (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar ALIVE da THRIVE, da MSF.