✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a magance matsalar tsaro a kasashen Musulmi

Wakilan da suka halarci taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmit Duniya (OIC) sun ce dole kasashen su hada kai tare da yin aiki da juna…

Wakilan da suka halarci taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmit Duniya (OIC) sun ce dole kasashen su hada kai tare da yin aiki da juna kafin su samu nasarar magance kalubalen ta’addanci da ke addabarsu.

Hakan na cikin muhimman batutuwan da wakilan kasashe 57 mambobin kungiyar suka tattauna tare da amincewa da su a karshen taron Majalisar Ministocin Harkokin Waje na Kngiyar karo na 47 da ya gudana a Niamey, Babban Birnin Jamhuriyar Nijar.

Ministocin sun koka cewa matsalar ta’addanci da kyamar Musulmi ita ce babbar matsalar da ke ci wa kasashen Musulmi tuwo a kwarya ta yadda ’yan ta’adda ke fakewada addini wajen bata sunan Musulunci.

Taron ya gudana ne a Babban Dakin Taro na Duniya na Mahatma Ghandi da ke birnin Niamey a ranakun Juma’a da Asabar, 27 da 28 ga watan Nuwamban bana.

Wakilan kungiyar sun amince su hada karfi da karfe ta hanyar taimakon juna wajen musayar bayanai da sojoji da tallafin kudade domin magance matsalar tsaro da ta fi shafar kasashen yankin Sahel da yankin Tabkin Chadi.

Da yake jawabi yayin bude taron, Babban Sakataren Kungiyar OIC mai barin gado, Dokta Yousef Al-Othaiminya ce taron na bana ya zo ne a daidai lokacin da aka fi bukatarsa. “Taron ya zo ne a daidai lokacin da kasashe masu yawa daga cikin mambobinmu ke fama da kalubalen tsaro da matsalar kyamar Musulmi musamman a Nahiyar Turai”, inji shi.

Ya kara da cewa, “Yawanci bata wa Musulunci suna kawai suke ba gyarawa ba”.

Kashi 82 na ta’addanci na shafar Musulmi ne —Issoufou

Da yake jawabi yayin bude taron, mai masaukin baki kuma Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou ya koka cewa fiye da kashi 82 cikin 100 na wadanda ayyukan ta’addanci ya fi shafa a duniya Musulmi ne.

Shugaban ya ce ya lura kalubalen tsaron da ke addabar kasashen Musulmi da dama ya yi matukar yi musu illa ta yadda akasarin kudaden kasafinsu a kowace shekara ke tafiya a batun harkar tsaro.

Ya ce, “Wannan ne lokacin  da ya kamata kasashen Musulmi musamman na yankin Sahel su hada karfi da karfe wajen magance kalubalensu ta bangaren sojoji da musayar bayanai.

“Sai dai ya zama wajibi shugabanni su farka tare da fahimtar cewa yaqi da talauci na taka muhimmiyar rawa wajen magance ta’addanci da kuma tsattsauran ra’ayin addini”, inji shi.

Ya koka kan yadda ’yan ta’addan ke shiga rigar addini wajen yin ta’asa, yana mai cewa ta’addanci ba ya da muhalli a Musulunci.

Shugaban ya kara da cewa taken taron na bana, “Hadin Kai Domin Yaki da Ta’addanci Don Samun Zaman Lafiya” ya zo a daidai lokacin da aka fi bukatarsa, musamman lura da kalubalen da kasashe mambobin kungiyar OIC ke fuskanta.