✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kece-raini a zaben Gwamnan Sakkwato

Duk da cewar ana jin duriyar ’yan takarar guda hudu, amma dai an fi jin jam’iyyun APC da PDP a jihar

A daidai lokacin da babban zaben Najeriya na shekarar 2023 ke karatowa, jam’iyyun siyasa a Jihar Sakkwato sun tsayar da ’yan takarar gwamna domin ganin an zabe su, lamarin da ya sa kowanensu yake shiga lungu da sako domin ganin hakarsa ta cim ma ruwa.

Sama da jam’iyyun siysa 10 ne a jihar suka tsayar da gwanayensu, amma an fi jin amon ‘yan takarar jam’iyya hudu, wato PDP da ta tsayar da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Malam Sa’idu Umar da aka fi sani da Malam Ubandoma.

Sai APC da ta tsayar da Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, sai NNPP da ta fito da Sanata Umar Dahiru Tambuwal da kuma ADP da tsayar da Malam Ibrahim Muhammad Liman Sifawa ne.

Duk da cewar ana jin duriyar ’yan takarar guda hudu, amma dai an fi jin jam’iyyun APC da PDP a jihar.

A kowace kakar siyasa akwai abin da take zuwa da shi da zai fi shahara, ko da kuwa an saba da shi a baya.

A wannan kakar ta bana, siyasar sauya sheka tsakanin manyan jam’iyyu biyu ce ta fi jan hankalin mutane, inda ake yawan samun masu sauya sheka a siyasar Jihar Sakkwato, sabanin siyasar baya.

Wasu manazarta siyasa a Sakkwato suna kallon wannan sauya shekar a matsayin kasuwar biyan bukata ce kawai ke ci, ba wani tagomashi na ’yan takara ba.

Hakan ya sa da yawan mutane ke nada kansu shugabancin karya a wasu mazabu ko kananan hokomomi a lokacin sauya shekar, inda sai bayan tafiyarsu shugabannin su fito suna karyata sauya shekar.

Masu sauya shekar na fakewa da cewar ’yan siyasar ba sa iya yin kowace irin hidima ga magoya bayansu sai wadanda suka sauya sheka, suka dawo jam’iyyarsu.

Wannan ne ya sa ‘yan siyasa suke yawan sauya sheka domin su samu abin da za su biya bukatunsu, inda a lokacin zabe kuma sun san wanda za su zaba.

Ahmad Aliyu: APC

Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto: Tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya zama Kwamishinan Jin-dadi da Walwala, inda daga bisani ya rike Ma’aikatar Lafiya a mulkin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Haka kuma ya zama Mataimakin Gwamna a Jihar Sakkwato a wa’adin farko na mulkin Aminu Waziri Tambuwal.

Ahmad Aliyu Sokoto

Ya samu gogewa daidai gwargwado, wanda ake ganin karkashin kulawarsa an samu ci-gaba.

Jam’iyar APC tana da wasu damarmaki da yawa da ake ganin za ta iya amfani da su domin karbe ragamar mulki daga PDP, duba da yanayin rashin zaman lafiya da jihar ke fama da shi a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Haka kuma wasu na ganin tazarar da Gwamna Tambuwal ya samu a zaben 2019 ba wani abin a-zo-a-gani ba ne.

Sai dai akwai batun cewa jam’iyyar APC mai mulki a kasa tana shan suka ganin matsalar tsaron da ake fama da shi a kasa da tsadar rayuwa, wanda hakan ya sa wasu suke ganin mutane za su bujire mata a zaben badi.

Haka kuma ana ganin APC kamar tana karkashin mutum daya ne, inda shi ne wuka, shi ne nama, wanda hakan ya sa ake ganin kamar zai iya zama wata barazana ga jam’iyyar.

Malam Sa’idu Umar: PDP

Malam Sa’idu Umar tsohon ma’aikacin banki ne da ya zama Kwamishinan Kudi, sannan ya zama Sakataren Gwamnati a mulkin Aminu Waziri Tambuwal.

Dan siyasa ne da ake ganin yana da kwarewa daidai gwargwado, inda magoya bayan PDP ke ganin duk nasarar da mulkin Tambuwal ya samu akwai hannun Malam Ubandoma ciki, don haka ya kamata ya gaji uban gidansa domin ci gaba daga inda ya tsaya.

Malam Sa’idu Umar

PDP ita ma tana da damarmakin da za su iya taimaka mata samun nasara, musamman karfin kasancewarta mai rike da kambun mulkin jihar, inda a lokuta da dama kayar da jam’iyyar mai mulki ke da wahala, sannan kuma jam’iyyar tana da magoya baya da yawa a jihar.

Sai dai kuma tana fuskantar rikicin cikin gida tsakanin tsagin Mataimakin Gwamna Maniru Dan’iya da ke ganin ba a yi musu daidai ba, kodayake wasu na ganin wannan ba wata matsala ba ce, za a shawo kanta.

Wasu ma suna ganin ko ba a shawo kanta ba, ba za ta shafi nasarar jam’iyyar ba, ganin yadda ta samu wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama da suka tsallako cikinta.