A mataki na farko na samun nagartacciyar mace shi ne, ka zama nagari. Matukar ka zama nagari, to ana sa ran za ka samu mace tagari.
A dabi’ar kowane mutum yana burin aurar mace tagari ko da shi ba nagari ba ne, domin kowa ya tabbatar da cewa mace tagari babbar alheri ce ga mijinta.
Akwai bukatar idan ka tashi neman aure, to ka tsaya ka yi zurfin tunani a kan wacce za ka aura, ka natsu ba a son gaggawa, kada ka biye kyale-kyalen duniya, ko wata karairaya da mace za ta yi maka, kada ka rudu da cewa mahaifinta mai hannu da shuni ne.
Ya dan uwa akwai bukatar ka lura da wadannan alamomin mace tagari kafin aure da suka hada da: ana so ta kasance mai tarbiyya, mai ilimi da aiki da shi, mai natsuwa da kamewa, ta kasance mai lizimtar addini, ta kuma kasance mai kunya.
Bayan an yi aure kuwa: ga alamomin da ya kamata ka duba kamar haka: Rashin yi wa miji gori, godiya da dawainiyar da yake yi mata, rashin kushe kokarinsa, rashin dora masa dawainiya da wahalhalu na babu gaira babu dalili. Sauran sun hada da yi wa miji biyayya karfafa shi a kan irin kokarin da yake yi, neman shawararsa a kan al’amuranki, rashin cutar da shi, girmama iyaye da ‘yan uwansa,
Haka babu laifi ka duba mace mai kyawu, ma’ana ka ce kai mai kyau za ka aura kana da damar yin haka, ba laifi ba ne, amma Musulunci ya hana aurar mace don zallar kyawunta ko yawan dukiyarta, inda Ma’aiki SAW ya ce: “Kada ku auri mace don zallar kyawunta ko dukiyarta ko nasabarta, ku dai ku auri ma’abociyar addini hannunka zai ribatu”
Wani kuma ya fi son baka, wankan tarwada, wani kuma shi duk yadda za a yi ya fi son fara kamar yadda a zamanin nan mutane da yawa suke raja’a a kai. Idan har ka samu duk wacce kake so din, to lallai kada ka sanya yaudara a ciki, yi kokari, ka gaya mata gaskiyar halin da kake ciki, ita ma ta gaya maka gaskiya, kada ka bari ta yaudare ka, kuma kai ma kada ka yaudare ta.
Lallai ka more! Kuma abin a yi maka murna ne samun mace tagari, domin duk wani dadin duniya da mace tagari ne yake tabbata, kuma matukar aka samu uwa tagari, to babu shakka za a samu ’ya’ya nagari, kasa kuma sai ta zauna lafiya, kwanciyar hankali da wadata su yalwata.
Ibrahim Hamisu Kabara ya rubutu daga Kano.
Za a iya samunsa a wannan lambar: 08060651676
Yadda za a gane mace tagari
A mataki na farko na samun nagartacciyar mace shi ne, ka zama nagari. Matukar ka zama nagari, to ana sa ran za ka samu mace…