Wata matashiya mai tuka jirgin sama a kasar waje, ’yar asalin Jihar Nasarawa, Adzuayi Ewuga, ta rasu sakamakon hadarin jirgin da take tukawa a Kasar Kamaru.
Marigayiya Adzuayi ta rasu ne bayan da dauko ma’aikatan kamfanin mai na a jirgi daga Filin Jirgin Sama na Yaounde Nsimalen zuwa Belabo da ke Gabashin kasar Kamaru, inda helikwaftan ya yi hadari, ita da fasinjojin gaba daya suka ce ga garinku nan.
- Gani ya kori ji: Hotunan muhimman abubuwa a wannan makon
- Mako mai zuwa muke sa ran ASUU ta dawo aiki —Gwamnati
Kyaftain Adzuayi tana tuka jirgin sama ne a kamfanin kamfanin Caverton Aviation da ke kasar Kamaru, ’yar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa kana tsohon Ministan Abuja, Sanata Solomon Ewuga, ce.
Shekara biyu nan da Najeriya ta rasa zaratan matasanta mata masu tuka jirgin sama, kuma dukkansu daga yankin Arewa ta tsakiya a sakamakon hatsari.
Rasuwar Kyaftain Adzuayi, ya girgiza jama’a da dama, musamman a jiharta ta Nasarawa.
Ta rasu kimanin shekara biyu bayan mace ta farko mai tuka jirgin soja na yaki, Tolulope Arotile mai shekara 23, ’yar asalin jihar Kogi, ta rasu, a wani hatsarin mota shekaarar 2020.
Tuni dai Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Kyaftin Adzuayi, wadda ya ce babbar asara ce ga Jihar Nasarawa da ma Najeriya baki daya.
Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun Babban Sakataren Yada Labarai ga Gwamna, Ibrahim Addra, ta nuna Gwamna Sule ya mika ta’aziyarsa ga iyaye da dangin marigayiyar.
Gwamna Sule ya ce, “A wannan lokaci da muke fuskantar jarrabawa, muna jajanta wa Sanata Ewuga da dangi da abokan arziki. Wannnan rashin ya shafi kowa saboda matashiyar matukiyar jirgin saman ta yi rayuwa abar koyi.
“Don haka muke addu’ar Allah Ya bai wa Sanata Solomon Ewuga da ahalinsa hakuri da juriyar wannan babban rashi,” in ji Gwamnan.