Rundunar Sojin Amurka ta sanar da cewa ta kammala kwashe dakarunta kakaf daga Afghanistan bayan shafe shekaru 20 tana gumurzu a ’yan Taliban wadanda ta kira masu tsattsauran ra’ayin addini.
Tuni dai ’yan Taliban suka karbe ikon kasar ta Afghanistan gaba daya, bayan da jirgin da ke dauke da rukuni na karshe na dakarun Amurka ya bar kasar.
- Janyewar Amurka: Ina makomar Afghanistan bayan kama mulkin Taliban?
- Kurunkus: Jirgin karshe dauke da dakarun Amurka ya bar Afghanistan
Hakan dai ya kawo karshen yakin da aka shafe shekara 20 ana fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Amurka ta tafi ta bar kungiyar na da karfi fiye da lokacin da ta shiga kasar a 2001.
An dai ji karar harbe-harben bindigogi na murna a birnin Kabul, yayin da wani bidiyo ya nuna mayakan kungiyar suna shiga filin jirgin saman kasa da kasa na Hamid Karzai bayan jirgin karshe na dakarun Amurka ya bar kasar da tsakar daren ranar Litinin.
Ga kadan daga cikin hotunan muhimman abubuwan da suka wakana a kasar bayan ficewar Amurkan: