✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’Yan Siyasa “Ke Mayar Da Matasa ’Yan Kwaya”

Ana zargin ’yan siyasa da gurbata wa matasa tarbiyya, da lalata musu makoma


Domin sauke shirin latsa nan

Idan kuna biye da mu a shirye-shiryenmu biyu da suka gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye, sannan muka duba wadanda ke amfana da harkar shaye-shayen a Najeriya. 

A wannan karon kuma mun mayar da hankali ne a kan  rawar da ake zargin ’yan siyasa na takawa wajen gurbata wa matasa tarbiyya, da lalata musu makoma ta hanyar saka su shaye-shaye don su cimma wata manufarsu ta siyasa.