Jami’an tsaron ‘yan sanda da suka samu rakiyar sojoji sun samu nasarar kashe Dan fashi 1 tare da kama 3 a garin Mpape Abuja inda ‘yan fashin suka kai hari bankin First Bank.
‘Yan sandan sun garzayo wajen ne, jim kadan bayan kai harin ‘yan fashin a bankin na First Bank da ke garin, a safiyar yau Asabar bayan samun labarin ‘yan fashin na kutsawa cikin bankin a Garin na Mpape.
Aminiya ta samu labarin cewa, ‘yan sandan sun yi amfani da hayaqi mai sa kwalla wajen tilastawa ‘yan fashin fita daga cikin bankin bayan sun shafe sa’o’i su na ta jiransu daga waje, ba tare da nasara ba.
Da farko dai uku daga cikin ‘yan fashin ne su ka fito inda jami’n tsaron su ka kashe daya daga cikin su.
Bayan wani lokaci sai su ka kama ragowar 2 daga cikin bankin tare da wani jami’in bankin daya da a ke zargi da hannu a lamarin da a ka same su tare.
Babbar mai magana da yawun rundunan ‘yan sanda ta Abuja ASP Mariam Yusuf, wadda ta tabbatar da faruwan lamarin, ta ce an wuce da mutanen 5 don fara bincike a kansu.