’Yan Najeriya sun nuna bacin ransu kan karin farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi daga N149 a ranar Laraba, wanda shi ne na uku a cikin wata uku.
Hukukumar Kula da Farashi Albarkatun Man Fetur (PPMC) a sanarwar da ta fitar ta ce daga dafo-dafon mai za su rika sayen litar fetur a kan N151.56.
“Sabon sauyin farashin albakatun mai da muke samarwa ya fara aiki. Saboda haka yanzu litar fetur ta koma N151.62”, inji sanarwar ta PPMC ga masu dafo-dafo.
Hakan ta sa Kungiyar Dillalai Mai Masu Zaman Kansu (IPMAN) ke batun cewa gidajen mai za su sayar da litar fetur a kan Naira 162, ko da yake Shugaban kungiyar na Kasa, Chinedu Okoronkwo, ya ce suna jiran isowar umarnin na PPMC.
- Gidajen mai za su sayar da litar fetur N162 —IPMAN
- Yadda ’yan Najeriya ke caccakar karin kudin wutar lantarki
- Buhari ya amince a kashe Dala biliyan 3.1 kan hukumar kwastam
Bincikenmu ya gano cewa har wasu gidajen mai sun kara farashin musamman a Legas, yayin da ’yan Najeriya ke caccakar karin, wanda ya zo a washegarin karin farashin wutar lantarki wanda shi ma ya fusata su.
Shugaban IPMAN na yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajudeen a wata hira da manema labarai ta waya a Abeokuta, Jihar Ogun, ya ce ba su da zabi face su sayar da litar man a kan Naira 162.
Sai Shugaban IPMAN a Jihar Kano, Alhaji Bashir Danmalam, ya ce suna tattaunawa kan farashin da za su sayar da fetur nan gaba.
Zuwa lokacin da wakilinmu ya kammala zagayen gidajen mai a Kaduna a ranar Larabar, ya lura ba su yi kara kudi ba.
– ’Yan Najeriya sun bayyana bacin rai –
Masu ababen hawa da motocin haya da ma’aikata da masu sana’o’i da sauran ’yan Najeriya sun bayyana takaicin karin kudin man.
“Bai dace ba saboda mutane na cikin wahala kuma babu aiki. Wannan karin zai takura jama’a sosai. Gwamnati ta daktar da shi’, inji wani direban haya a Legas, Ojo Gabriel.
Shi ma Ikechukwu Ebekwe ya koka cewa an yi karin kwana guda bayan kara farashin wutar lantarki, yayin da hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 15 cikin 100.
Wata wadda wakilinmu ya yi hira da ita a Abuja, Maryam Abdullahi, ta ce karin zai tsananta wahalar da masu karamin karfi ke ciki.
Masu ababen hawa a tashoshin mota na Jabi da Utako a Abuja sun ce kara farashin fetur din ya nuna gwamnati ba ta damu da mutane ba.
“Muna kokarin farfadowa daga kullen COVID-19; al’amura ba su gama kankama ba amma gwamnati ta rasa abin da za ta yi sai karin kudin mai”, inji Okay Micheal, wani direban haya a Abuja.