Wani yaro mai kimanin shekara 10 ya gamu da fushin wasu ’yan kasuwa da ake zargi sun babbake shi bisa zargin sa da satar shinkafar da zai ci tare da mahimaifinsa.
’Yan kasuwan sun dade suna zarin yaran da satar kayan abincinsu da suka hadar da garin rogo yana kaiwa gida.
Majiyarmu ta ce yaron ya rasa mahaifiyarsa tun yana dan karami kana mahaifinsa na fama da lalurar tabin hankali lamarin ya sa yake zuwa kasuwar kauyensu a Karamar Hukumar Ohaukwu a Jihar Ebonyi yan fakar idon ’yan kasuwar ya debi dan abin da zai ci da mahaifin nasa.
Mazauna sun ce wasu ’yan kasuwa ne suka daure yaron suka jefa shi cikin sharar da suka kunna wa wuta bayan ya yi yunkurin dibar shinkafa a wata rumfa.
Shugaban kungiyar kare hakki ta HURIDE reshen Jihar Ebonyi, George Etamesor ya nuna bacin ransa kan cin zarafin da ’yan kasuwan suka yi wa yaron.
Yace yadda suka jefa yaron cikin wuta suka gasa tamkar akuya saboda ya yi yunkurin dibar danyar shinkafa ya saba doka da ka’ida.
“Wasu mutanen yankin ne suka kai wa yaron dauki suka kai shi asibitin AMURT da ke Effium inda likitoci ke kokarin ceton ransa domin yana cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
“Mutanen ne suka ankarar da kungiyarmu ta kare hakkin dan Adam domin bi wa yaron hakkinsa.
“Mun kuma je domin jin ta bakin wadanda suka yi masa aika-aikar inda suka shaida mana cewa yaron ya saba yi musu dauke-dauken kayan abinci, yana fakar ido ya saci rogo, garin kwaki ko doya.
“Saboda haka da suka kama shi yana dibar danyar shinkafarsu sai suka yi mishi danyen hukuncin.
“A fadarsu, ba da niyyar su kone dukkan jikinsa suka sa shi a wutar ba, sun saka shi ne domin kone diga-diginsa domin kada ya sake takowa zuwa wajen ya yi sata, amma da suka saka shi a wutar sai ya yi ta birgima a wutar ya kone duka jikinsa, ganin haka yasa suka sanarwar wa ’yan sanda”, inji shi.
Kakakin ’yan sanda a jihar Ebonyi, Loveth Odah ta ce ba a shigar wa rundunar karar ba a rubuce, amma ta samu labarin aika-aikan.
“Za mu kama mutanen da suka yi wa yaron ta’asar domin su fuskacin shari’a.
“Kungiyar kare hakkin dan Adam ta HURIDE ta ankarar da mu amma ban ji dadin yadda suka ce kada mu kama mutanen a yanzu ba sai nan gaba, saboda yanzu su ke biya wa yaron kudin magani” inji ta.
Ta ce ba ta san hujjar kungiyar ba na cewa a dakatar da kama mutanen ba.