✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ‘yan Kannywood suka gabatar da addu’oin zaman lafiya

A ranar Litinin ne ’yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka gudanar da taron addu’o’i na musamman a karkashin kungiyar 13×13 ta mawaka wacce Alhaji…

A ranar Litinin ne ’yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka gudanar da taron addu’o’i na musamman a karkashin kungiyar 13×13 ta mawaka wacce Alhaji Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta.

An gudanar da taron ne a Jihar Kano, inda aka yi saukar alkurani aka kuma yi addu’o’i domin zaman lafiya.

Taron ya samu halartar manya da kuma kananan ‘yan masana’antar mata da maza, gami da tsoffi da sabbin jarumai da kuma sauran ma’aikata.

Ga wasu hotunan yadda taron ya kasance:

Wasu dadga cikin alarammomi suna saukar kur’ani a taron (Hoto: Maikatanga)
Shugaba kuma wanda ya dauki nauyin taron addu’ar Dauda Kahutu Rarara (Hoto: Maikatanga)
Auwalu Mashal da Habibu Yaro, da Shehu Hassan Kano, da Kabiru Maikaba da Rarara a taron (Hoto: Maikatanga)

Saratu Daso da Lubabatu Madaki, da Safiya Kishiya, da Zakiyya da kuma sauran jarumai mata a taron (Hoto: Maikatanga)

 

Adamu Kwabon Masoyi, Abduillahi Zakari Ligidi wasu tsaffin jarumai a masana’atar (Hoto: Maikatanga)
Hussaini Sule Koki da Mustapha Mijinyawa tare da Abdullahi Mohammed a wurin taron (Hoto: Maikatanga)
Fati Al Amin da Rabi Sufi da sauran wasu jarumai a mata a taron (Hoto: Makatanga)

 

Hadiza Gabon da Ibrahim Birniwa, Aisha Tsamiya tare da wasu jarumai a taron addu’ar. (Hoto: Maikatanga)

 

Malam Nata’ala da Auwalu BB Hotoro da wasu dattawan masana’antar a taron (Hoto: Kabir Maikaba)
Jarumi Tanimu Akawu a wurin Taron

 

Karin wasu dattawan masana’antar da suka halarci taron (Hoto Maikatanga)
Mawaki Billy O da kuma Faruk Sayyadi a taron (Hoto Bill O)
%d bloggers like this: