Sojojin Najeriya sun kashe ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB hudu gabanin zaben Gwamnan Jihar Anambra da ke tafe.
Sojojin sun bindige ’yan IPOB din ne a musayar wuta da suka yi a Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a jihar, sojoji suka murkushe su.
- ‘Sakacin mahukunta ke haifar da yawan fasa gidajen yari’
- Sojojin Najeriya sun kashe masu kera bom din Boko Haram
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun aika bata-garin lahira ne bayan sun kai hari kan jami’an tsaro a Karamar Hukumar Aguata ta Jihar Anambra.
Ya ce bayan samun labari ne sojojin suka bi sawunsu, suka kashe hudu a musayar wuta, a hanyar Nnewi zuwa Nnobi suka kwace makamansu, amma soja daya ya rasa ransa.
– Sojoji sun dakile harin ’yan IPOB
Nwachukwu ya ce sojoji sun kuma dakile wani harin IPOB a wani shingen bincike a Karamar Hukumar Orumba ta Kudu a jihar.
Ya ce nan take sojoji suka fatattaki bata-garin, suka cika bujensu da iska suka zubar da makamansu da wasu daga cikin ababen hawansu.
A cewarsa, hare-haren wata dabara ce ta ’yan IPOB ta razana mutane domin kar su fito kada kuri’a a zaben gwamnan jihar da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa.
Amma “Sojoji da sauran jami’an tsaro na ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa za su murkushe duk tsagerun da ke neman razana su.
“Ana bukatar daukacin jama’a masu bin doka su ci gaba da harkokinsu yadda suka saba cikin kwanciyar hankali, sannan su kai wa cibiyar tsaro mafi kusa da su rahoton duk wani take-taken da ba su gamsu da shi ba.”
Idan ba a manta ba Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno, a wani zama da aka yi da hukumar zabe (INEC) kan shirye-shiryen zaben Gwamnan Anambra ya gargadi masu neman tayar da hargitsi da su shiga taitaiyinsu.
Bayan zaman ne Gwamnatin Tarayya ta tura kwamandojojin ’yan sanda na musamman guda 100 domin tabbtar da tsaro a fadin Jihar Anambara.