✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan fim ke fama da talauci bayan ɗaukaka

Ba a Kannywood kaɗai ake samun irin wannan matsala ba, har da Masana’antar Nollywood ta Kudancin Nijeriya.

Idan ba a manta ba a bara ce, Aminiya ta rawaito yadda fitaccen dan wasan Hausa, Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Karkuzu ya makance, inda ya fito a wani faifan bidiyo yana neman taimakon a saya masa gida.

Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya gwangwaje shi da gida da kudin abinci da sauransu, inda fitaccen dan wasan ya kashe kusan Naira miliyan 5.5.

Sai dai duk da haka, idonsa bai bude ba, domin a bidiyon ya bayyana cewa, cutar glaucoma ce, wadda ba a warkewa.

Kafin wannan, Aminiya ta ruwaito lokacin da fitaccen jarumin barkwanci, Bashir Bala Ciroki ya yi fama da talauci, inda ya fito yana neman taimako.

Haka kuma akwai irin su Sani Idris Moda da marigayi Sani SK da duk suka sha fama da jinya, inda a karshe ma aka yanke kafar Sani Moda.

Wannan lamari ya sa ake ganin ba a samun kuɗi a harkar fim kuma ga dukkan alamu duk bula ce kawai a harkar.

Idan ba a manta ba, akwai lokacin da aka shiga rudani a Masana’antar Kannywood, bayan dattijuwa kuma jarumar masana’antar, Ladin Chima ta shaida wa sashen Hausa na BBC cewa, a wani lokacin ma takan samu Naira 2,000 kudin fitowa a fim.

A lokacin maganar ta tayar da kura a masana’antar, inda Ali Nuhu da Darakta Falalu Dorayi da wasu manyan furodusoshi suka kalubalanci jarumar, wadda ta dade tana harkar.

A lokacin ne Naziru Sarkin Waka ya fito ya ce, “… Gaskiyar magana ’yan fim ba Allah a ransu.

“Duk wadanda suka yi magana a kan matar nan babu Allah a ransu kwata-kwata. Yanzu saboda Allah, Ali Nuhu da Falalu Dorayi za su ce ba su san ana daukar Naira 2,000 ko Naira 1,000 ana bai wa tsofaffin nan idan sun tashi daga fim ba? Ku ji tsoron Allah mana, kowa ya san masana’antar nan (Kannywood) tana fama da matsaloli daban-daban,” in ji shi.

Aminiya ta gano cewa, yawancin jarumai, musamman masu tasowa suna hakuri ne da kuɗi kadan kafin su girma.

Wannan na cikin dalilan da wasu suke amfani da shi wajen tambayar ina jarumai ’yan mata suke samun kudi?

Haka kuma, Aminiya ta ruwaito yadda fitattun jaruman masana’antar, wadanda aka dade ana damawa da su suke zuwa karbar tallafin da manyan jaruman masana’antar suke rabawa, musamman mawaki Dauda Kahutu Rarara da Abdul Amart Maikwashewa.

Shin a Kannywood kawai matsalar take?

Binciken Aminiya ya gano cewa, ba a Kannywood kaɗai ake samun irin wannan matsala ba, har da Masana’antar Nollywood ta Kudancin Nijeriya, inda can ma matan sukan fi wasu fitattun mazan samun dukiya.

Kwanan nan wani faifan bidiyo na jarumin Nollywood Amaechi Muonagor ya fito, inda a ciki aka nuna shi a wani yanayi mara kyau na rashin lafiya, yana neman tallafin kudi.

A bidiyon, an gan shi kwance kan gado da bandeji a kirjinsa, yana magana da kyar.

Wani dan fim da ke zaune kusa da shi yana ce, Muonagor yana bukatar kudi domin a yi masa aikin dashen koda.

A bidiyon da aka fitar ranar Litinin, Muonagor cikin damuwa, yana magana da harshen Ibo, inda yake cewa: “Al’ummar Ibo, ina gaishe ku baki daya,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Bai iya karasa magana ba, sai jarumi Kingsley Orji ya ci gaba da bayani yana cewa, jarumin yana fama da matsalar koda.

“Babu sauki. Ya shafe watanni yana cikin wannan yanayi. Yana son a yi masa dashen koda,” in ji Orji.

Ya ce, “Mun yanke shawarar mu mayar da shi gida saboda babu kudi, amma hakan ba shi ne ya fi dacewa ba. Da kyar yake iya magana. Don Allah yana bukatar taimakonku.”

Muonagor ya yi finafinai da dama har da Aki da Paw Paw, daya daga cikin finafinan da ya taka rawa sosai, inda ya fito a matsayin mahaifin matasan biyu.

Wannan na zuwa ne ’yan makonni bayan rasuwar fitaccen jarumi John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu, wanda ya shahara wajen barkwanci, ta yadda ba ma ya bukatar bude baki kafin sa mutane dariya.

Jarumi Mista Ibu ya sha fama da jinya, inda daga bisani aka yanke masa kafa, amma kuma bayan wani lokaci ya ce ga garinku nan.

Mista Ibu ya rika neman taimakon jaruman masana’antar domin ya samu damar neman magani, inda suka tara masa kudi mai yawan gaske.

Haka ma fitaccen mawaki Eadris Abdulkareem, wanda ya yi fice da wakarsa ta Nigeria Jaga-Jaga, ya sha fama da ciwo, har sai da aka tara masa kudin jinya.