Mutum hudu sun rasu a wani fashi da makami aka yi a kauyen One-Man Village da ke kusa da Mararaba a Jihar Nasarawa, mai makwabtaka da Babban Birnin Tarayya.
Maharan dauke da bindogi sun shammaci jami’an tsaro da masu sayayya ne a Wisdom Supermarket, da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi a Jihar Nasarawa a ranar Talata.
A yan kwanankin nan dai an samu kuwarar ayyukan bata-gari a yankunan da ke kusa da Abuja, inda ake wa jama’a fashi ko garkuwa da su, wani lokaci ma a kashe su, bayan masu garkuwa da su sun karbi kudin fansa.
Wanda ya auku a kauyen One-man a ranar Talata shi ne na baya-bayan nan da ’yan fashi suka nuna tsaurin ido.
- Hatsarin ayarin Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kashe ’yan tawagarsa
- Hisbah ta kama mota maƙare da kwalaben barasa dubu 24 a Kano
- An kama likitar bogi kan zargin kashe mai juna biyu a Kano
Ko da wakilinmu ya ziyarci yankin a ranar Laraba, ya iske al’umma suna tattauna abin da ya faru.
Wasu daga cikinsu sun shaida masa cewa abin da suka gani a babban shagon kasuwancin, kamar a mafarki ne, lura da lokacin da aka kai harin.
Wani dan yankin ya shaida wa wakilin namu cewa da misalin karfe 8.30 na dare ’yan fashin suka shiga wurin, a daidai lokacin da ake tsaka da hada-hadar kasuwanci, suka rika bincika ko’ina suna neman a ba su kudi.
Wani ganau mai suna Mista Adamu Jacob, ya koka da cewa masu laifi na cin karensu babu babbaka a kusan ko’ina a fadin Abuja da wasu sassan jihohin Nasarawa da Neja da ke makwabtaka da ita ba tare wani kwakkwaran mataki daga jami’an tsaro ba.
Wani mai aikin gadi a wani wuri da ke kusa da inda abin ya faru ya ce ’yan fashin da suka yi aika-aikan sun rufe fuskokinsu.
“Na ga dayansu a tsallaken hanya. Da shigarsu ciki sai suka yi wa jama’a tsawa suka kwakkwantar da su a kasa.
“Abin takaici, haka suka gama abin da za su yi suka tafi,” in ji shi.
Wata wadda ta tsallake rijiya da baya a fashin mai suna Talatu Musa, ta ce tana dab da shiga wurin sai ta ji an fara harbe-harbe, shi ne ta ce ‘kafa me na ci ban ba ki ba’.
Talatu Musa, ta ce, “wani gidan mai da ke kusa da wurin na shige na boye, ina tunanin abin da zai samu na cikin wurin.
“Sai daga baya na ji abin da ya faru a radio, shi ya sa na dawo tare da mijina domin mu yi musu ta’aziyya.”
Talatu ta yi kira a sauya salon aikin ’yan sanda a cikin jama’a domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyi.
Kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ranham Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, har ya ce, ana gudanar da binciki.
DSP Nansle ya ce, bayan samun rahoto, jami’ansu sun je wurin, “da isarsu sun samu gawarwakin mutum hudu da aka harbe.
“An kai mutanen asibiti inda likita ya tabbatar sun rasu, sannan aka sanya su a dakin ajiyar gawa domin bincike.”
Dubban mutanen da ke aiki a Abuja suna zaune ne a wajen garin ko a sassan Jihar Nasarawa.
A baya-bayan nan dai mazauna Abuja na cikin tashin hankali saboda karuwar hare-haren ’yan bindiga da ke yawan yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Wani sabon salo da maharan suka dauka shi ne na kai hari a kusa da manyan birane ko a cibiyoyin kasuwanci a rana tsaka kamar yadda suke yi a jihohin da ke makwataka da Abuja irin su Neja, Nasarawa, Kogi da Kaduna.
Kafin yanzu ’yan bindiga sun fi yin irin wannan ta’asa ne a yankunan karkara, inda suke satar kayan abinci da dabbobi da sauran dukiyoyi da ma mutane domin karbar kudin fansa.
Ko a ranar Talatar nan sun kai hari a yankin Garam a Jihar Neja, wanda ke kusa da Makarantar Aikin Lauya da ke Bwari a Abuja.
Ba a jima ba, a kwanakin baya mahara kusan 1,000 a kan babura dauke da muggam makamai sun raba kimanin mutum 2,000 da muhallansu a sakamkon wani hari da suka kai a yankin Adagba da ke Yaba, Karamar Hukumar Abaji a yankin Birnin Tarayya.