✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin ayarin Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kashe ’yan tawagarsa

Motar jami'an tsaro a tawagar mataikin gwamnan ta yi adungure a lokacin da suke hanyar zuwa mahaifar mataimakin gwamnan.

Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Mataimakin Gwamna Sakkwato, Idris Gobir, inda hakan ya ’yi ajalin wani dan sanda da wani mai daukar hoto a tawagar.

Mutanen biyu sun gamu da ajalinsu a wannan hatsari ne bayan wata motar jami’an tsaro a cikin tawagar mataimakin gwamnan ta kwacce sannnan ta yi adungure a yankin  Yanrimawa da ke kan hanyar Goronyo-Sabon Birni

Hatsarin ya auke ne a lokacin da mataimakin gwamnan da ayarin nasa suke kan hanyarsu ta zuwa mahaifarsa, Sabon Birni a ranar Laraba.

Injiniya Idris ya tafi kauyen nasu ne domin kabar bakuncin Gwamna Ahmed Aliyu da zai kai ziyarar ta’aziyya a yankin.

Darakktan yadaa labaran mataimakin gwamnan, a tabbatar da rasuwar dan sandan da ke tuka motar da kuma wani mai daukar hoto  da ke ciki motar.

A cewarsa an kai gawarwakin dakin ajiyar gawa.

A lokacin da muka samu wannan labarin dai kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i ya ce ba shi da labari wannan hatsari.