Zauna-gari banza sun kai hari a dakin ajiyar ababen hawan da hukuma ta kwace a Abuja inda suka kwashe daruruwan babura da ke ajiye a wurin.
Matansa sun fake ne da zanga-zangar #EndSARS suka fasa dakin ajiyar da Ofishin Kula da Lafiyar Ababen Hawa (VIO) ke kula da shi a unguwar Gosa.
- #SecureNorth: Dalilin dakatar da zanga-zanga —Bulama
- Zanga-zangar #EndSARS na iya kara tsadar kayayyaki — Masana
Daraktan VIO na Abuja, Wadata Aliyu Bodinga ya ce sun sanar da ‘yan sanda kuma sun kawo musu dauki nan take, amma matasan suka fi karfinsu.
“Mun gode Allah babu wani jami’inmu da ya samu ko da rauni a lokacin da mutanen suka mamaye wurin namu”, inji Bodinga.
Wani shaida ya tabbatar wa Aminiya cewa daruruwan matasan unguwanni masu makwabtaka da Gosa sun yi wa wurin tsinke a Yammacin Litinin, suka rika daukar babura suna tafiya da su.
Majiyarmu ta ce an yi ta tara baburan a wurin ne tun lokacin da aka haramta baburan haya aiki a kwaryar birnin Abuja.
Wata majiyar na cewa daga lokaci zuwa lokaci akan yi gwanjon baburan hayan da aka kwace ga masu saye daga wasu jihohi.