Mayakan kungiyar Boko Haram sun rika yin kwanton bauna suna farautar malamai a garin Geidam na jihar Yobe, har suka kashe uku daga cikinsu.
Biyu daga cikin wadannan malaman an kashesu ne ta hanyar harbi a Makarantar Fasaha ta Gwamnati dake Geidam, dayan kuma ya gamu da ajalinsa ne a gidansa.
- Ranar ma’aikata: Buhari ya jefa ’yan Najeriya cikin tsaka mai wuya – Atiku
- Gobara ta hallaka masu COVID-19 18 a cibiyar killacesu a Indiya
Ba a dai ambato sunan wadanda aka kashe din ba, amma shaidu sun bayyana yadda ’yan ta’addan suka jima suna cin karesnu ba babbaka a garin.
Rahotanni sun nuna cewa sun rika yin kokarin dibar sabbin matasa da nufin shigar dasu kungiyar ta Boko Haram.
Gidaje da dama mallakin ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa ne ’yan ta’addan suka rika bankawa wuta bayan sace kayan cikinsu sannan suka rika rabawa talakawa.
Kazalika, kayayyakin kamfanonin waya suma sun fuskanci hari, lamarin da ya sa mazauna garin suka shiga tsaka mai wuya wajen neman taimako kafin su fara yin hijira.
Mamayar ta Boko Haram dai ta tilasta wa dubban mazauna garin yin hijira zuwa makwabtan garuruwa domin neman mafaka.
Yawancinsu dai sun ce ba za su taba mantawa da mamayar ta kwanaki biyar ba.
Aminiya ta rawaito cewar gungun mayakan sun mamaye garin ne a kan motocin yaki sama da 20 ta gabashin garin bayan sun ci karfin sojoji.