✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 62 a Zamfara da Sakkwato

’Yan bindiga sun kara kawo hari a yayin da ake shirin yin jana'izar mutanen da suka kashe

Ana fargabar ’yan bindiga sun hallaka mutum 62 a hare-haren da suka kai a yankunan jihohin Zamfara da Sakkwato.

Akalla mutum 37 ne ake zargin ’yan bindiga sun kashe baya ga wasu da dama da suka jikkata a kauyuka uku na Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato, inda suka kara kawo hari a yayin da ake shirin yin jana’izar mutanen da suka kashe.

A Zamfara kuma ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 25, ciki har da ’yan banga 16, a yankin Kanoma da ke karamar Hukumar Maru, da wasu mutum biyu a Karamar Hukumar Maradun.

An kai hare-haren ne a ranar Asabar, kwana biyu bayan ganawar Shugaba Boka Tinubu da shugabannin tsaron kasa, inda ya umarce su da su hada karfi tare da ɗaukar sabbin matakai na bai-daya wajen tabbatar da tsaron kasa.

Da yake tabbatar da harin, Shugaban Karamar Hukumar Tangaza,  Bashar Kalenjeni, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindiga sun kashe muyun  18 a kauyen Raka da wasu 17 a kauyen Raka Dutse sai wasu biyu a kauyen Filingawa.

“Mun yi kokarin yi musu jana’iza a ranar da dare, amma ’yan bindigar suka sake dawowa suka fatattaki kowa,” in ji shugaban karamar hukumar.

Aminiya ta gano cewa a yammacin ranar Lahadi aka samu aka yi jana’izar mutanen, bayan da aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.

Shugaban karamar hukumar ya ce wasu da dama da suka samu ranunin harbi ana jinyar su a Babban Asibiti da ke  Gwadabawa.

Ya ce, ’yan bindiga sun kai musu harin ne saboda jama’ar kauyukan sun ki ba su kudaden harajin da suka kakaba musu.

“’Yan bindiga sun sanya musu haraji da suka so ya fara aiki nan take, tare da zaba musu abin da za su yi, amma mazauna yankunan suka bijire, shi ne suka kashe musu mutum 37.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Rufa’i Ahmad, ya tabbatar da harin, amma suna jiran cikakken rahoto daga babban ofishinsu da ke kula da yankin.

A lokacin, ya ce suna daji tare da sojoji kuma zai tuntubi wakilinmu daga baya kan abin da ya faru, sai dai har zuwa lokacin da aka kammala wannan labarin hakan bai samu ba.

Wani mazaunin gairn Gidan Madi, hedikwatar Karamar Hukumar Tangaza, Kabiru Gidan Madi ya tabbatar da maganar shugaban karamar hukumar game da harajin da ’yan bindiga suka wajabta musu.

’Yan bindiga sun zagaye kauyukan

“Dajin Tsauna ya tafi daga Gwadabawa zuwa Illela har zuwa Jamhuriyar Nijar sai kuma Dajin Kuyanbana da ya bi ta Gudu ya bulla Jamhuriyar Nijar. A dazukan suke buya saboda tsaunukan da ke ciki.

“A Kuyanbana akwai wasu da ake kira Lakurawa masu alaka da mayakan jihadi daga kasashen Nijar da Mali da Libya.

“Da farko ba sa kai wa kauyuka hari, wa’azi kawai suke mana su koma; sun ma sha kai wa ’yan bindiga hari su kwato mutanen da suka sace, kafin daga baya suka fara satar dabbobi, amma ba sa kashewa ko sace mutane.

“Dajin Tsauro kuma ana zargin yawancin ’yan bindigar da ke cikinsa daga Nijar suke, inda suke kai wa kauyuka hari su kashe mutane, su sace wasu da dabbobin, sannan su koma kasarsu.

“Da farko, ’yan bididiga da Lakurawa ba sa shiri, amma yanzu sun hade, wanda hakan ya sa shiga wuraren ke wa jami’an tsaro wuya.

“Idan sojoji suka kai wa musu hari a Dajin Tsauro, sai su tsere ta Dajin Kuyanbana, idan a Dajin Kuyanbana ne kuma, sai su tsare ta Dajin Tsauro,” in ji shi.

Harin Zamfara

A harin Zamfara, ’yan bindiga a kan babura sun kashe sama da mutum 20 a kauyen Janbako, da wasu biyar a kauyen Sakkida.

“Sun shigo da misalin karfe 2 na rana suna harbi kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya sa kowa ya tsere; Daga baya suka shiga kauyen Sakkida suka kashe mutum biyar; An riga an binne wadansu daga cikin wadanda aka kashe,” in ji wani dan yankin mai suna Buhari Saminu.

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya yi tir da harin ya kuma yi alkawarin gwamnatinsa ba za ta zura ido ana kashe jama’ar jihar ba.

Gwamnan ta hannun mashawarcinsa kan yada labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ya “Umarci hukumomin tsaro da ke jihar, da su gaggauta tura karin jami’asu zuwa yankunan domin kare rayuka da dukiyoyi.”

Kokarinmu na samun kakakin ’yan sandan Zamfara,  ASP Yazid Abubakar, ya ci tura, amma ya fitar da wata sanarwa cewa a ranar Asabar din, rundunar ta kubutar da kananan yara tara ’yan kauyen Gora Namaye da ke Karamar Hukumar Maradun daga hannun ’yan bnidiga.

Ya ce, “’Yan bindiga sace yaran ne a lokacin da suke je daji neman icen girki, amma bayan samun rahoto rundunar ta yi nasarar cetowa da kum adamka yaran ga iyayensu, tana kuma ci gaba da kokarin kamo ’yan ta’addan.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Sojoji da ’yan sanda suna ci gaba da sintiri domin hana maimaituwar haka a yankin.”

 

Daga Sagir Kao Saleh, Abubakar Auwal (Sakkwato) & Shehu Umar (Gusau)