Hare-haren ’yan bindiga ya tilasta wa mazauna kananan hukumomin Gudu da Tangaza a jihar Sakakwato guduwa su kyale harkokin nomansu su gudu Jamhuriyar Nijar don gujewa yin garkuwa da su.
’Yan bindigar dai sun mamaye garuruwan ne inda suka rika karbar kudade daga mazauna yankunan suka kuma tilasta musu bayyana musu masu hannu da shuni wadanda za su iya yin garkuwa da su.
A tattanaunawarsa da Sashen Hausa na BBC a ranar Litinin, daya daga cikin mazauna kauyen Kurdula ya ce kullum da yamma mata da kananan yara kan shiga halin kaka-ni-ka-yi saboda sun san a lokacin ne maharan ke kai ziyartar su.
Ya ce da dama daga cikinsu yanzu sun koma yin hijira domin kwana a Jamhuriyar Nijar sai washe-gari da safe su dawo.
“Lamarin da muka tsinci kanmu a kananan hukumomin Gudu da Tangaza abin ban tsoro ne. kullum da daddare sai mahara sun ziyarce mu gida-gida da bindigogi.
“Idan ba ka da kudi sai su tilsta maka ka nuna musu mai kudin da za su iya yin garkuwa da shi. Ko jiya sai da suka sace mutum biyu wadanda har yanzu ba su sakko ba saboda ba a biya musu diyya ba.
“Da zarar Magriba ta yi mata da kananan yara suke fara kuka saboda ba su san inda za su sa kansu ba. Kusan dukkan masu kudin garin nan yanzu sun koma Nijar,” inji shi.
Ya ce matukar kana da abinda ya kai N30,000 ba kai ba kwanciyar hankali a yankin, yana mai cewa yanzu ’yan bindigar kan nemi mazauna kowanne kauye su hada musu kudade muddin suna so su zauna lafiya.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati kan ta taimaka ta kawo musu dauki daga maharan.
Sai dai Kwamishinan Tsaron jihar, Kanal Garba Moi Isa mai ritaya ya shaida wa BBC cewa sun sami gagarumar nasara a yakin da suke da maharan.