✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka yi barna a Kaduna

Mutum biyu sun mutu wasu 20 kuma an yi garkuwa da su a harin da ’yan bindiga suka kai a jihar Kaduna. Maharan sanye da…

Mutum biyu sun mutu wasu 20 kuma an yi garkuwa da su a harin da ’yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.

Maharan sanye da kayan jami’an tsaro, sun kafa shingen binciken ababen hawa kafin su yi aika-aikan a yankin Sabuwar Kaduna da ke Karamar Hukumar Chikun.

“Sun zo sanye da kayan sojoji da ’yan sanda suka kafa shingen binciken ababen hawa a daidai gadar shiga unguwar, suka yi ta tsayar da masu ababen hawa”, inji wani mazaunin yankin, mai suna Kasimu Keke.

Ya ce direbobi da yawa sun tsaya domin sun zaci jami’an tsaro ne, amma da wani mai shagon ya yi kokarin tserewa da ya yi zargin cewa ’yan fashi ne sai suka harbe shi.

“Sun kuma kashe wani karin mutum daya”, inji shi.

Mazauna yankin sun ce ’yan fashin sun sa shingen binciken nasu ne a kusa da gabar shiga yankin Sabuwar Kaduna, da misalin 8.00 na daren Lahadi.

%d bloggers like this: